1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar dattijan Amirka ta yi wani taro na musamman don tattauna batun yakin Iraqi.

Majalisar dattijan Amirka, ta yi wani taro na musamman a asirce, wanda aka dade ba a yi irinsa ba, don angaza wa fadar White House ta cika alkawarin da ta dauka na kammala binciken da aka fara kan zargin da ake yi mata na yin jujjuya rahotannin leken asiri wajen hujjanta dalilanta na afka wa Iraqi da yaki .

Wakilan majalisar, na jam’iyyar Democrats, sun cim ma nasara a gwagwarmayar da suke yi na tilasa wa masu tsara dokokin yin muhawara a kan wannan batun. Su ko `yan jam’iyyar Republicans, sun yi Allah wadai da wannan matakin, amma sun amince da kafa wani kwamiti, wanda zai ba da rahotonsa kafin ran 14 ga wannan watan, a kan yadda binciken zargin da ke yi wa fadar White House din ke ci gaba.