1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar dattijan Amirka ta amince da fadada shingen kan iyaka da Mexico

Majalisar dattijan Amirka ta amince da kasafin dala miliyan 70 a matsayin kudaden da aka ware na aikin gaggawa ga sojojin Amirka a Iraqi da Afghanistan. Hakan ya sa kasafin da aka warewa ma´aikatar tsaron Amirka a badi zuwa dala miliyan dubu 450. Dukkan wakilan jam´iyun democrats da republicans da yanzu suka dukufa wajen yakin neman zaben ý an majalisun dokoki da za´a yi cikin watan nuwamba, sun kada kuri´ar amincewa da wannan kari, bayan da majalisar wakilai ta amince da wannan mataki tun da farko. A wani labarin kuma majalisar dattijan ta Amirka ta amince da da wani shirin fadada shingen kan iyakar Amirka da Mexico, a wani mataki na yaki da kwararar bakin haure dake shiga Amirka. Fadada shinge da kilomita kusan dubu 1 zai kara tsawon sa da kashi daya cikin uku a iyakar kasashen biyu mai tsawon kimanin kilomita dubu 10.