Majalisar dattawan Amurika ta yi Allah wa Iran Allah wadai | Labarai | DW | 17.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar dattawan Amurika ta yi Allah wa Iran Allah wadai

Majalisar dattawan Amurika ta kada kuri´ar amincewa da yin Allah wadai da kasar Iran, bayan shawaran da ta yanke na ci gaba da sarrafa makamn nuklea.

Sanarwar da Majalisar ta hiddo, ta zargi Iran da sabawa dokokin kasa da kasa na hana yaduwar makaman nuklea.

Yan majalisar Dattawan Amurika, sun bada goyan baya, ga kasashen da ke bukatar gurfanar da Iran gaban komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia.

A wani huruci da ta yi jiya sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, ta dangata Iran, da mattatara yan ta´ada na dunia.

Sai dai kamar yada zaman dunia ya gana wani ya ki ka wani ya so ka , ita kasar Cuba cewa, tayi matsayin da Iran ta dauka yayi daidai.