Majalisar Dattawan Amurika ta amince da tura dakarun NATO a yankin Darfur | Labarai | DW | 04.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Dattawan Amurika ta amince da tura dakarun NATO a yankin Darfur

Majalisar dattawan Amurika ,ta bada haɗin, kai ga matakin tura dakararun shiga tsakaini, na ƙungiyar tsaro ta NATO, kokuma OTAN,a yankin Darfur, na ƙasar Sudan.

Kakakin Majalisar, ya ba shugaba Bush na Amurika, damar tantanawa da takwarorin sa, na ƙasashe membobin ƙungiyar NATO , da kuma kungiyar taraya Afrika,domin cimma matakin bai ɗaya.

Sadidai majalisar Dattawan Amurika, ta shawarci cewa, wannan runduna ,ta yi aiki ƙarƙashin dakarun ƙungiyar taraya Afrika da ta ƙunshi sojoji dubu 7, wace ke yankinDarfur tun shekara da gabata, amma har yanzu, ta kasa shawo kan rikicin sanadiyar ƙarancin kayan aiki.

Ranar alhamis da ta wuce, ministan tsaro na ƙasar Sudan, ya nuna adawa da tura sojojin shiga tsakani daga ƙasashen turai, ko Amurika, a yankin Darfur.

Har ma ya ƙara da barazanar cewa, Darfur za ta zama ƙabburburan wannan sojoji, muddun a ka tura su.

Shima wakilin mussamn na Majalisar Ɗinkin Dunia,a Sudan, ya bayyana haɗarrurukan da ke tattare, da aika rundunar ƙungiyar Nato a yankin Darfur.