Majalisar datawan Amurika ta amince da ci gaban ayyukan sojojin Amurika a Irak | Labarai | DW | 16.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar datawan Amurika ta amince da ci gaban ayyukan sojojin Amurika a Irak

Majalisar dattawan Amurika, ta rataba hannu a kan dokar amincewa, da ci gaban ayyukan sojojin Amurika a ƙasar Iraki.

Hatta da yan ɓangaren demokrate, sun yi na´am da wannan mataki, wanda a cewar yan majalisar, ke matsayin nuna goyan baya, ga samar da zaman lahia a ƙasa da ke fama da tashe-tashen hankula.

To saidai sun bukaci a gudanar da cenje-cenje, ta yadda za a samu cimma nasara, a kann burin da aka sa gaba.

Shugaba Georges Bush, da ke shan suka a game da yaƙin na ƙasar Irak, ya bayyana gamsuwa, da haɗin kann da ya samu, daga yan majalisa.

Amincewa da wannan doka, ya zo daidai lokacin da ƙarin sojojin Amurika 4, su ka rasa rayuka a cikin hare-hare a birnin Bagadaza.

Daga fara wannan yaƙi ya zuwa yanzu, a jimilce sojojin Amurika 3.200 a ka bayana cewar sun sheƙa lahira.