1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Majalisar Bundestag ta yi muhawara kan girke dakarun Jamus a Jumhuriyar Dimukraɗiyya ta Kwango

Majalisar Dokokin Jamus, wato Bundestag, ta fara muhawara a kan girke dakarun rundunar sojin Bundeswehr a Jumhuriyar Dimukraɗiyya Ta Kwango. Ministocin gwamnati da wakilan jam'iyyun adawa sun yi ta bayyana ra'ayoyinsu a kan shirin. Yayin da ɓangaren gwamnatin ke kira ga majalisar ta yi amanna da shirin, jam'iyyun adawa na FDP da kuma na 'yan gurguzu na watsi da shirin ne gaba ɗaya, inda suke zargin gwamnatin da rashin tsara wa Afirka kyakyawan shiri.

Taron majalisar dokoki ta Bundestag a birnin Berlin

Taron majalisar dokoki ta Bundestag a birnin Berlin

Girke dakarun Jamus a birnin Kinshasa da kewayensa, wani nauyi ne da kuma kasada da gwamnatin tarayya za ta iya ɗauka, saboda kyautatuwar halin tsaro da aka samu a yankin babban birnin, inji ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier. Ministan, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga taron majalisar dokoki ta Bundestag, don tattauna shawarar da gwamnatin tarayya ta yanke ta tura dakarun rundunar soji ta Bundeswehr zuwa Jumhuriyar Dimukraɗiyya Ta Kwango. Ya kara da cewa, bai kamata Turai ta juya wa Majalisar Ɗinkin Duniya da al’umman Kwangon baya ba, a lokacin da suka nemi taimako daga gare ta. Babu shakka, al’umman Kwangon dai na bukatar samun wata dama, ta sake gina ƙasarsu, inji shi.

A cikin nasa jawabin, ministan tsaro na tarayya Franz Josef Jung na jam’iyyar CDU, ya bayyana cewa, an cika duk ƙa’idojin da ake bukata na tura dakarun zuwa Kwango:-

„An dai cika duk ƙa’idojin da suka dace na girke dakarun a Kwangon, bayan da gwamnatin tarayya ta amince da yin hakan, sa’annan kuma wasu kasashe 18 na Turai, su ma suka yi amanna da ba da tasu gudummowa ga shirin. Sabili da haka ne nake ganin cewa, za mu iya ɗaukar wannan nauyin, kuma mun kammala duk shirye-shiryenmu. Ya cancanta dai mu bayyana gaban wannan majalisar, don mu nemi amincewarta ga shawarar da gwamnati ta yanke.“

A cikin nata jawabin a muhawarar da aka yi, ministan ma’ammalar tattalin arziki da ba da taimakon raya ƙasashe ta tarayya, Heidemarie Wieczoreck-Zeul, ta jam’iyyar SPD, ta yi watsi da zargin da wasu masharhanta ke yi wa nahiyar Turai, na cewa ƙasashen EU da sauran ƙasashe masu ci gaban masana’antu, na wannan ɗawainiyar ne kawai saboda sha’awar da suke da ita, ta kwashe albarkatun ƙasa a sawwaƙe daga Kwangon. Ta dai nanata cewa:-

„Afirka maƙwabciyarmu ce. Kuma nauyin bai wa nahiyar agaji ya rataya a wuyarmu, musamman idan an bukace mu mu yi haka ɗin. Wannan dai wata dama ce da muka samu a yanzu, ta ba da tallafi, wanda kuma ba shi da wata alaƙa da launin fata. Ina nanata hakan ne kuwa, saboda na ji wasu gunagunai a lokacin wannan muhawarar.“

Jam’iyyar adawa ta Greens, ita ma ta ce tana goyon bayan shirin. Kakakin jam’iyyar a kan batutuwan da suka shafi harkokin ƙetare, Jürgen Trittin, ya ce jam’iyyarsa na goyon bayan amsa kiran da gwamnatin tarayyai ta yi, ga neman taimako da al’umman Kwangon da Majalisar Ɗinkin Duniya suka miƙa wa ƙungiyar EU. Bisa cewarsa dai:-

„Wannan ɗaukin da za mu yi, yana da kasada, kamar dai duk wani ɗauki na girke dakaru a ƙetare. Amma abin tambaya a nan shi ne, wace irin moriya zai janyo mana, zai kuma janyo wa duniya baki ɗaya? Wajibi ne a kashe kuɗi fiye da dola miliyan 20 a kan wannan ɗaukin, ko kuwa zama za mu yi kawai mu sa ido mu ga kuma yadda babu shakka shirye-shiryen zaɓen zai ci tura, idan bam u taimaka ba? A nawa ganin dai yin hakan, wato rashin ɗaukar nauyin da ya rataya a wuyarmu ne.“

Sauran jam’iyyun adawa na FDP da jam’iyyun gurguzu a majalisar dai sun yi watsi da shirin ne ma gaba ɗaya. Kakakin jam’iyyar FDP a kan batutuwan da suka shafi harkokin tsaro, Birgit Homburger, ta zargi gwamnatin tarayya ne da gaza fito da wani tsari na tabbatad da tsaro da zaman lafiya mai ɗorewa a nahiyar Afirka.

 • Kwanan wata 19.05.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btzy
 • Kwanan wata 19.05.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btzy