Majalisar al´umar China ta fara taron ta na shekara shekara a Beijing | Labarai | DW | 05.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar al´umar China ta fara taron ta na shekara shekara a Beijing

A China an bude zaman taron majalisar al´umar kasa na wannan shekara. A jawabin sa na bude taron na kwanaki 12 a birnin Beijing FM Wen Jiabao ya yi kira da a dauki nagartattun matakan kare muhalli da yin tsimin makamashi. FM ya ce dole kasarsa ta samu bunkasar tattalin arziki na kashi 8 cikin 100 a bana. Wakilai kima´nin dubu 3 dake halartar taron zasu albarkaci wasu sabbin dokoki biyu wadanda zasu share fagen kara sakarwa harkokin kasuwancin kasar mara. Sabuwar dokar mallakar kadarori a China ta tanadi ba da cikakkiyar kariya iri daya ga kamfanoni masu zaman kansu da na gwamnati. A dangane da haka ana shirin kafa wata sabuwar dokar biyan haraji wadda zata soke wani rangwami da ake yiwa masu zuba jari na ketare. Tabbas taron zai amince da karin kasafin kudin na kashi 18 cikin 100 ga ayyukan soji.