Majalisar Ɗinkin Duniya zata kaddamar da Gidauniyar tallafi | Labarai | DW | 11.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Ɗinkin Duniya zata kaddamar da Gidauniyar tallafi

Amurka za ta bada karin tallafi wa yankunan ambaliya a Pakistan

default

Majalisar Ɗinkin Duniya za ta kaddamar da Gidauniyar neman tallafi domin taimakawa miliyoyin al'ummar Pakistan da ambaliyar Ruwa ta ritsa da su. Babban sakataren Majalisar Ban ki Moon ya ce, ana bukatar tallafin miliyoyin daloli domin agazawa yankunan da matsalar ta shafa. A halin da  ake ciki dai Amurka ta sanar da karin gudummowar dala miliyan 20, domin taimakawa waɗanda suka fuskanci matsalar ambaliyar. Mutane 1,600 ne dai suka rasa rayukansu, ayayinda wasu miliyan 14 suka kasance cikin hali mawuyaci. A ranar talata nedai shugaban Paskistan Asif Ali Zardari ya komo daga balaguronsa a nahiyar Turai, inda ake cigaba da sukansa da nuna halin rashin kulawa dangane da bala'in ambaliyar Pakistan din mafi muni cikin shekaru 80.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Edita :Umaru Aliyu