Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira ga kawo ƙarshen hare-hare a Darfur. | Labarai | DW | 09.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira ga kawo ƙarshen hare-hare a Darfur.

Babbar jami’ar kula da harkokin kare hakkin ɗan Adam na Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kakkausar suka ga gwamnatin ƙasar Sudan, inda take zarginta da yunƙurin sauya daidaiton da ake da shi na ƙabilun yankin Darfur. A cikin wani rahoton da ta gabatar, jami’ar Louise Arbour, ta ce binciken da hukumarta ta gudanar na nuna cewa gwamnatin Sudan na bi ta kan mayaƙan sa kai wajen kai manyan hare-hare a kan matsugunan fararen hula a kudancin yankin Darfur. A wani harin da aka shafe kwanaki huɗu a jere ana yi, rahoton ya ce ɗaruruwan fararen hula ne suka rasa rayukansu. Jami’ar dai ta ce rahoton na dogaro ne kan tambayoyin da aka yi wa waɗanda suka tsira da rayukansu daga hare-haren da aka kai wa yankin, a cikin watannin Agusta da Satumba da suka wuce. Sabili da haka ne take kira ga girka wata kafa mai zaman kanta a Sudan ɗin, don ta gudanad da cikakken bincike, sa’annan kuma a gabatad da duk waɗanda aka same su da laifin gudanad da wannan ɗanyen aikin gaban shari’a. Har ila yau dai jami’ar ta kuma yi kira ga mahukuntan birnin Khartoum da su taimaka wajen jigilar kayayyakin agaji da magunguna zuwa yankunan da ake bukatansu cikin gaggawa a kudancin Darfur.

Tun shekara ta 2003 dai, a ƙalla mutane dubu ɗari 2 ne suka rasa rayukansu, sa’annan fiye da miliyan biyu kuma suka ƙaurace wa matsugunansu, saboda fafatawar da ake yi a yankin na Darfur.