Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa, wani bala’in ƙarancin abinci na barazanar kunno kai a Afghanistan. | Labarai | DW | 25.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa, wani bala’in ƙarancin abinci na barazanar kunno kai a Afghanistan.

Hukumar Tallafa wa Duniya da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ta yi gargaɗin cewa, idan ba a samo taimakon agaji daga ƙetare ba, kusan mutane miliyan ɗaya ne za su huskanci barazanar ƙarancin abinci a Afghanistan. Darektan reshen Asiya na Hukumar, Anthony Banbury ne ya bayyana haka, inda kuma ya ƙara da cewa, ɓarkewar yunwa, zai iya sa mafi yawan ’yan ƙasar su goyi bayan aƙidar ƙungiyoyin da ke yaƙan gwamnati. A wata fafatawar da sojojin gwamnatin Afghanistan ɗin tare da goyon bayan jiragen saman yaƙin dakarun ƙetare, suka yi da mayaƙan Ƙungiyar Taliban a kudancin ƙasar yau, rahotanni sun ce mutane da dama a cikinsu har da fararen hula ne suka rasa rayukansu.