Majalisar ɗinkin Duniya ta yi ƙara kan harin jami′anta a Sudan | Labarai | DW | 09.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar ɗinkin Duniya ta yi ƙara kan harin jami'anta a Sudan

Majalisar ɗnkin Duniya ta gabatar da ƙara gaban gwamnatin Sudan bayan ta ce dakarun gwamnati sun yi wa jami’an tsaronta da ke yankin Darfur kwantar ɓauna. Majalisar ɗinkin Duniya ta ce wani direbanta farar hulla ya ji munanar raunuka a wannan harin da ya auku da yanmacin litinin, karon farko da jami’anta ke fuskantar hare-hare tun bayan tsugunar da rundunar a yankin Darfur. Jami’an hadin-gwiwar Majalisar ɗinkin Duniya tare da na kungiyar Tarayyar Afirka na maye gurbin jami’an AU da ke fama da ƙarancin kayyakin gudanar da tsaro, amma Sakatare Janar Ban Ki-Moon ya ce rundunar na buƙatar hadin kai daga gwamnatin Sudan. Ita kuma gwamnati ta mayar da martanni da cewar jami’anta sun kai wannan harin bisa kuskuren cewar ‚yan tawaye ne.