1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Ɗinkin Duniya na neman AU ta ci gaba da girke dakarunta a yankin Darfur.

Babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan, ya ce yana ƙoƙarin ganin cewa, an tsawaita wa’adin girke dakarun kare zaman lafiya na Ƙungiyar Tarayyar Afirka, wato AU, a yankin Darfur har zuwa ƙarshen wannan shekarar, yayin da a wani ɓangaren kuma, ake ta hidmiomin cim ma yarjejeniya kan maye gurbinsu da dakarun Majalisar Ɗinkin Duniya. Da yake yi wa taron maneman labarai jawabi a taron ƙoli na Ƙungiyar AUn da ake yi a birnin Banjul na ƙasar Gambiya, Kofi Annan, ya ce ya bukaci shugabannin ƙasashen ƙungiyar da su nuna sassauci ga shirinsu na janye dakarun a ƙarshen watan Satumba, saboda rashin kuɗin da suke huskanta.

Ana dai kyautata zaton cewa, kafin rufe taron yau, shugabannin za su yanke shawara kan matakan da za a ɗauka nan gaba game da yankin na Darfur, inda yaƙin basasa da aka shafe shekaru 3 ana yi, ya janyo asarar rayukan mutane fiye da dubu ɗari 3.