Majalisar Ɗinkin Ɗuniya tace Sudan tana karan tsaye ga tura dakaru Darfur | Labarai | DW | 28.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar Ɗinkin Ɗuniya tace Sudan tana karan tsaye ga tura dakaru Darfur

Shugaban rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce Sudan tana ci gaba da yin karan tsaye ga yunƙurin tura dakarun wanzar da zaman lafiya a lardin Darfur.Jean Marrie Guehenno ya ce kaidoji da Sudan din ta ginadaya suna kawo cikas ga tabbatar da tura dakarun.Cikin bukatun na Sudan a cewarsa sun haɗa da miƙa mata tsarin irin aiyukan rundunar da gurare da zasu yi sintiri.Jean Marrie ya kuma yi soki gwamnatin Sudan da laifin toshe duk wata kafa ta shigar da wasu kasashe cikin rundunar.yace ba zai yiwu su gudanar da aiyukansu ƙarkashin irin wadannan kaidoji ba.