1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Ɗinkin Duniya ta kwatanta jefa bamabamai masu tarwatsewa da Isra’ila ta yi a Lebanon da aikin masha’a.

August 31, 2006
https://p.dw.com/p/Bukv

Babban jami’in kula da ba da taimakon agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya, Jan Egeland, ya yi kakkausar suka ga jefa bamabamai masu tarwatsewa da Isra’ila ta yi a Lebanon, kwanaki uku kafin ƙaddamad da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta. Jami’in ya ce wannan wani ɗanyen aiki ne na masha’a. Ya kuma yi gargaɗin cewa akwai ɓaraɓusai kusan dubu 10 na bamabaman, waɗanda ba su fashe ba tukuna, suna tarwatse a ko’ina a kudancin Lebanon, inda kuma za su kasance wata babbar barazana ga rayuwar jama’a a yankin. Abin ban takaici, wanda kuma ya zo daidai da aikin masha’a dai shi ne, inji jami’in, jefa kusan kashi 90 cikin ɗari na bamabaman da Isra’ila ta yi a cikin sa’o’i 72 kafin a ƙulla yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar. Kamar dai yadda ya bayyanar:-

„Abin ɓacin rai, ko ma, abin da zan iya kira aikin masha’a shi ne ganin cewa, an jefa kashi 90 cikin ɗari na bamabamai masu tarwatsewar ne, a cikin sa’o’i 72 kafin kawo ƙarshen rikicin, wato a lokacin da kowa ya san cewa za a cim ma yarjejeniya, lokacin da muka san cewa za a zo ga ƙarshen fatatawar.“