Majalisa ta tsige shugabar Koriya ta Kudu | NRS-Import | DW | 09.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Majalisa ta tsige shugabar Koriya ta Kudu

'Yan majalisar adawa da na gwamnati sun albarkanci kudirin tsige shugabar kasa Park Guen-Hye daga mukaminta bisa dalilan cin hanci da karbar rashawa.

'Yan majalisar dokokin Koriya ta Kudu sun amince da kudirin tsige shugabar kasa Park Geun-Hye bisa zargin badakalar cin hanci da karbar rashawa da ta shafa mata kashin kaji. Daukacin 'yan majalisa na bangaren adawa da 'yan Independa da kalilan na jam'iyar da ke mulki ne suka albarkacin wannan mataki na yankar kauna. Makonni da dama sun Koriya ta Kudu suka shafe suna zanga-zanga da nufin tilasta wa shugabar mai shekaru 69 sauka daga karagar mulki, amma ta yi buris ta bukatar tasu.

Firaministan Koriya ta Kudu ne zai yi rikon kwarya kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada. Sai dai kuma Park Geun-Hye zata ci gaba da rike mukaminta har sai kotun tsarin mulkin Koriya ta Kudu ta tabbatar da matakin da majalisa ta dauka, lamarin da zai iya daukan watanni shida. Ita dai Geun-Hye ta kasance shugaba ta farko da aka tube a tarihin Koriya ta Kudu.