1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisa a Faransa ta amince da dokar zaman baki

Majalisar dokokin Faransa ta amince da wata sabuwar doka wadda zata tsaurara zaman baki a cikin kasar. To sai dai kafin dokar ta fara aiki dole sai majalisar datijai ta albarkace ta. A cikin watan yuni ake sa rai majalisar dattijan zata yi muhawwara tare da jefa kuri´ar akan sabúwar dokar wadda zata takaita zaman tare da shige da ficen baki a cikin kasar ta Faransa. To amma dokar zata saukawa baki masu kwarewa a sana´o´i dabam dabam neman izinin zama cikin kasar. Tuni dai kungiyoyin kare hakkin bil Adama da na kyautata zaman baki a Faransa ke ta gudanar da zanga-zangar yin tir da wannan doka.