1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mai yiwuwa an halaka Ayman al-Zawahiri a Pakistan

January 14, 2006
https://p.dw.com/p/BvCO

Kafofin yada labarun Amirka sun rawaito cewar watakila an halaka mataimakin shugaban kungiyar al-Qaida Ayman al-Zawahiri a wani farmaki da jiragen saman yakin Amirka suka kai kan wani kauye a Pakistan. Tashar telebiji ta ABC ta rawaito majiyoyin sojin Pakistan na cewa watakila Zawahiri na daga cikin kusoshin kungiyar al-Qaida su biyar da aka kashe a wannan hari. Ita kuwa tashar NBC ta rawaito majiyoyin ma´aikatar tsaron Amirka na cewa an kai harin ne da nufin halaka Zawahiri, wanda Amirka ke tuhumarsa da hannu a hare haren da aka kai kan ofisoshin jakadancin Amirka a wasu kasashen Afirka a shekarar 1998. Wani jami´in hukumar leken asirin Pakistan ya ce za´a gudanar da bincike akan gawawwakin kafin a tabbatar da asalin su. Kawo yanzu dai gwamnatocin Amirka da Pakistan ba su tabbatar da cewar ko farmakin wanda yayi sanadiyar mutuwar akalla mutane 17 na da alaka da fatattakar mayakan kungiyar al-Qaida.