Mahukuntan Amurka sun kalubalancin bashin da ake bin Najeriya | Siyasa | DW | 09.01.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mahukuntan Amurka sun kalubalancin bashin da ake bin Najeriya

Masu hankoron soke bashi da wasu yan majalisar Amurka sun roki Shugaba Bush da ya mayarwa Najeriya bashin da Amurka take binta

default

Membobin majalisar dokokin Amurka su 18 suka rattaba hannu akan wata wasika zuwa ga sakataren baitumalin Amurka John Snow da kuma shugaban bankin kula da shige da fice James Lambright suna masu bukatar gwamnatin Amurkan ta mayarda wani bangare na dala biliyan 24 da digo 4 da ya kamata Najeriya ta biya daga nan zuwa watan maris a matsayin wani bangare na yarjejeniyar rage mata bashi da ta cimma tsakaninta da paris Club a bara.

A watan Oktoba ne masu bada basusuka na kungiyar Paris club suka amince yafe dala biliyan 18 cikin dala biliyan 34 da ake bin Najeriya bashi.

Wani bangare na yarjejeniyar shine,Najeriya ta amince biyan dala biliyan 12.4 cikin watanni 6,wadda tuni ta biya kashin farko na dala miliyan 6.3,saura kuma zata biya a watan maris mai zuwa.

Sai dai mahukuntan Amurka sun ja da cewa,ya kamata gwamnatin Amurkan ta mayarwa da Najeriya wadannan kudade saboda dalilan jin kai,musamman ma tunda kudin da Amurkan take bin Najeriya dala miliyan 396 kadan ne.

Wasikar tace,a namu raayi,bai kamata ba Amurka ta karbi wannan kudi ,ganin cewa Najeriya tana daya daga cikin kasashe dake fama da talauci a duniya,ta kara da cewa,yafe wannan bashi ba wani abu bane cikin kasafin kudin Amurka mafi girman tattalin arziki a duniya,idan aka kwatanta da irin taimakon da kudin zaiyiwa Najeriya.

Yan majalisar na Amurka,wadanda Donald Payne na jamiyar republican da kuma Maxine Waters na jamiyar democrats suke jagoranta,sunce kashi 20 cikin dari na yaran Najeriya basa rayuwa zuwa shekaru 5,akalla yara 2,500 kuma suke mutuwa a kowace rana daga cututtuka da zaa iya karewa,yayinda wasu Karin 300,000 suke mutuwa a kowace shekara sakamakon cutar kanjamau.

Kudin da Amurka take bin Najeriya bashi bai taka kara ya karya ba inji su,idan aka kwatanta da wadanda kasashen Burtaniya,Italiya,Faransa da Jamus suke binta.

Karkashin shawarwarin yan majalisar,kudaden da zaa yafewa Najeriyar,ya kamata tayi anfani da su wajen rage radadin talauci,ta hanyar zuba su cikin aiyukan jin kai da bankin duniya zai dauki nauyinsu.

A farkon wannan wata ne,kungiyoyi da dama masu zaman kansu da suka hada ActionAid,Oxfam,Islamic Relief da Christian Aid suka rubutawa Tony Blair na Burtaniya irin wannan wasika,suna masu rokonsa da ya dauki matakan yafewa Najeriya bashin,suka ce mafi yawa na kudaden da Najeriya zata biya,aljihun gwamnatin Burtaniya zasu tafi.

Wadda suka ce wannan yana nufin cewa,cikin yan watanni kadan masu zuwa kudaden da Najeriya zata biya Burtaniya zasu nunka kudaden da Burtaniyan ta bayar na taimako ga dukkan nahiyar Afrika a 2005.Hakazalika zasu fi yawan gudumowa da Burtaniyan zata bayar ga shirin yafe basusuka na kungiyar G8 ga kasashe 18 matalauta cikin shekaru 30 masu zuwa.

A lokacinda batun yafe bashin na paris Club ya taso,kungiyoyi dabam dabam,sunyi suka ga shirin,suna masu cewa Paris club bata yi laakari da cewa mafi yawan basusukan Najeriyar, kudaden ruwa ne na basusukan da tsoffin shugabannin mulkin danniya na Najeriya suka karba a baya.

Hakazalika suma yan majalisar na Amurka sunce,mafi yawa na basusukan Najeriyan shugabaninta ne na baya suka karba suka kuma sace,yayinda kuma ruwa ke ta taruwa a kansu.

Kungiyoyin sun yi suka ga kaidojin da Paris Club ta baiwa Najeriya,suna masu cewa,kaidojin zasu tilastawa Najeriya tsara shirye shiryen tsuke aljihu karkashin kaidojin hukumar bada lamuni ta duniya.

Sau da yawa jamaa suna zargin IMF da laifin kafa tsauraran manufofin tattalin arziki ga kasashe dake karbar bashi,amma wadanda suke adawa da yafe bashin musamman daga kan Najeriya,sunyi nuni da cewa,ya kamata Najeriyar ta iya biyan basusukan da ake binta da kudaden rara na man fetur da take samu,musamman ma da yanzu farashin danyen mai yake ci gaba da hauhawa a kasuwannin duniya.

Najeriyar dai memba ce ta Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur na duniya.

 • Kwanan wata 09.01.2006
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu2b
 • Kwanan wata 09.01.2006
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu2b