Mahukunta a Kwango sun saki 'yan fafutika
December 27, 2016Talla
'Yan fafutika 19 da aka kamasu lokacin zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Joseph Kabila a Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango an sakesu a ranar Talatan nan, kamar yadda kungiyoyi da jami'an Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana.
Kungiyar Lucha ta tabbatar da cewa mambobinta 18 an sako su bayan da aka kamasu lokacin wani zaman dirshan da suka yi ranar 21 ga watan Disamba a birnin Goma da ke a Gabashin na Kwango, kamar yadda Ghislain Muhiwa wani fitaccen dan fafutika ya bayyana a ranar Talatan nan. Ita ma Gloria Senga, da aka yi garkuwa da ita a ranar 18 ga watan Disamba an saketa a cewar dan fafutikar.