1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahmud Ahmadinejad ya isa birnin Kampala domin neman goyon baya

April 23, 2010

A wannan makon ne shugaban Iran ya ƙaddamar da rangadin aiki a ƙasashen Zimbabwe da Uganda

https://p.dw.com/p/N57b
Hoto: AP

Shugaba Mahmud Ahamadinejad na Iran na cigaba da rangadi a ƙasashen Afirka, domin neman haɗin kai dangane da yunkurin Majalisar Ɗunkin Duniya na  kakaba wa ƙasarsa sabbin takunkumi, rage mayar da Iran saniyar ware tare da inganta dangantakar tattalin arzikinta.

Ƙasashen Zimbabwe da Ugandan da shugaban Iran ɗin ke ziyarta dai, suna da rawa da za su taka.

Iran dai na fuskantar suka daga ƙasashen yammaci na Turai, dangane da ci gaba da bunkasa sinadran Uranium da take yi wanda tace domin  makamashi ne. Ƙasashen turan dai na tsoron cewar, Iran ɗin na ƙera makaman ƙare dangi ne. Iran na fatan shawo kan Uganda da ke da kujera a komitin sulhu, wajen ƙin amincewa da ƙaƙaba mata sabbin takunkumin.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Edita: Umaru Aliyu