Mahmud Abbas zai kiri zaɓen raba gardama | Labarai | DW | 06.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahmud Abbas zai kiri zaɓen raba gardama

Shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, ya jagoranci wani mahimmin taro, da komitin zartaswa, na ƙungiyar PLO, a game da batun ƙuri´ar raba gardama, da ya ambaci shirya wa a ƙasar , da zumar jin ra´ayin jama´a, a kan hanyoyin warware rikici tsakanin Palestinu da Isra´ila.

Manyan jami´an Palestninu, na ɓangarori daban daban, da ke kulle a gidajen kurkukun Isreala, su ka gabata da wassu mattakai, wanda a tunanin su, za su samar da zaman lahia, tsakakin ƙasashenn 2, to saidai gwamnatin Hamas, mai tsatsauran ra´ayi, ta yi watsi da wannan shawarwari.

A taƙaici wannan kundi, ya shawarci dakatar da kai hare hare, ga Isra´ila, da kuma amincewa da iyakokin shekara ta 1967, da su ka raba ƙasashen 2.

Hakan na nufi, a fakaice amincewa, da ƙasar Isra´ila, batun da gwamnatin Hamas ke adawa da shi.

A sakamakon taron na yau, ƙungiyar OLP ta baiwa Mahamud Abbas goyan baya,wajen shirya wannan zaɓe.

Abbas ya yanke shawara shirya ƙuri´ar, jin ra´ayin jama´ar, a sakamakon taƙƙadamar da aka fuskanta, a tantanawa tsakakin Hamas da Fatah, da sauran ɓangarorin ƙasar, na tabatar da kwanciyar hankali, da kuma warware matsalolin takunkumin da ƙasashen Turai da Amurika su ka sakawa Paletinu.