1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahmud Abbas ne kadai wanda Isra´ila zata iya tuntuba, inji Peres

May 22, 2006
https://p.dw.com/p/BuxL

Mataimakin FM Isra´ila Shimon Peres ya bayyana shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da cewa shi ne mutum daya tilo da Isra´ila zata iya tattauna batun wanzar da zaman lafiya da shi a wannan lokaci da muke ciki. Wadannan kalaman da Mista Peres wanda memba ne a majalisar ministocin Isra´ila, ya yi a yau litinin sun saba da furucin da FM Ehud Olmert yayi jiya, inda ya kwatanta Mahmud Abbas da cewa ba ya da karfi da kwarjini kuma yayi rauni ta yadda ba zai iya aiwatar da duk wata yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya da banagrorin biyu zasu kulla ba. Peres ya fadawa gidan radiyon Isra´ila cewa Abbas ne kadai mutumin da za´a iya tattaunawa da shi amma ba wani dabam ba. Peres ya ce tun da ba za´a iya zama kan teburin sulhu da Hamas ba, Mahmud Abbas ne kadai wanda za´a iya tuntuba. A halin da ake ciki FM Isra´ila Ehud Olmert ya isa kasar Amirka inda zai tattauna da shugabannin kasar.