Mahmud Abbas a Berlin | Siyasa | DW | 01.02.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mahmud Abbas a Berlin

Shugaban Palesdinawa Mahmud Abbas ya gana da shugaban gwamnati, Angela Merkel a Berlin

default

Mahmud Abbas da Angela Merkel a Berlin

A bayan Piraministan Israila, Benjamin Netanyahu, da shugaban kasa Shimon Peres, shima shugaban Palesdinawa, Mahmud Abbas ya kawo ziyara a birnin Berlin. Lokacin ganawa da shugaban gwamnati, Angela Merkel yau, Abbas ya sanar da ita matsayin sa a game da rikicin yankin gabas ta tsakiya.

Ba dai wani boyaiyen abu bane sain cewarf shugaban na Palesdinawa, Mahmud Abbas, yana ganin shawarwarin neman zaman lafiya a gabas ta tsakiya sun mutu gaba daya yanzu, ko da shike shugaban Palesdinawan bai fito fili ya fadi hakan ba, a lokacin ziyarar sa a Berlin. Yanzu fiye da shekara guda kenan babu wani abibn da aka yi ta hanyar shawarwari tsakanin Palesdinawa da Israila. Fatan da Palesdinawan suka dorawa hawa mulkin shugaban Amerika, Barack Obama bai tabbata ba. Shima manzon Obama na musmaman a gabas ta tsakiya, Gerorge MItchell, ya zuwa yanzu, ya kasa samun nasarar kawo karshen abubuwan dake hana ruwa gudu tsakanin bangarorin biyu. Saboda haka ga Abbas babu abin da ya rage illa baiyana fatan watarana za'a koma shawarwarin na zaman lafiya. Yace

"Ba ma bukatar komawa ga daukar makamai. Muna adawa da gwada karfi irin na Intifada, mun kuma yi imani da samun sulhuta hanyar shawarwari. Idan har Israila ta dakatar da manuifofin ta na gina matsugunan Yahudawa a yankunan da ta mamaye na wani dan lokaci, ta kuma nuna shirin komawa ga tattaunawa yadda aka tsara, to kuwa a shirye muke mu shiga shawarwari da ita".

Palesdinawa suna bukatar Israila ta koma ga tsarin da aka yi tun farko na kasa da kasa, game da neman zaman lafiya, ko kuma Road Map a takaice, abin da ya hada har da dakatar da giggina matsunan Yahudawa a yankunan gabashin birnin Kudus da yammacin kogin Jordan. Sai idan hakan ya samu ne Palesdinawan zasu koma teburin shawarqwari da ita. A halin yanzu, Abbas yana nazarin wata shawara da manzon musmman na Amerika, George Mitchell ya gabatar, wanda da farko ta tanadi fara shawarwari na kananan jami'an Israila da Palesdinawa. Shugaban gwamnatin Jamus Angela Merkel tana ganin hakan yana iya zama wata hanya mai amfani ta cimma biyan bukata, saboda:

"Ta wannan hanya ko wane bangare yana iya nunar da bukatun sa, yadda za'a yi nazarin su, tare da fatan samun ci gaba. Abin da zan fadi a zahiri shine, ni kaina zan yi marhabin da hakan."

Nuna goyon baya ga tsarin nan na samun yantattun kasashe biyu, wato Israila da yantacciyar kasar Palesdinawa kafada da kafada da juna, yana daga cikin abubuwan da aka saba ji, a duk wata ganawa tsakanin Merkel da abokan tataunawar ta daga gabas ta tsakiya. To sai dai Palesdinawan suna kara nesa da cimma burin su na samun yantacciyar kasa a yanzu, fiye da a ko wane lokaci a tarihin yankin. Duk da haka, a wnanan yanayi mai wahala, Jamus tace zata taimakawa Palesdinawan a game da bunkasa tattalin arziki da raya yammacin kogin Jordan. Dangane da haka ne za'a kirkiro kwamitin hadin gwiwa na Jamus da Palesdinawa. Ga mazauna yankin Gaza dake fama da wahaloli sakamakon yake-yake da toshewar da Israila tayi masu, gwammnatin Jamus tace zata bada gudummuwar man fetur da tashoshin karfin lantarkin yankin zasu yi amfani dashi. Shugaban gwamnati, Angela Merkel tace mummunan halin da mazauna yankin suke ciki, ya zama abu mai kawo matukar damuwa.

Mawallafi: Umaaru Aliyu

Edita Zainab Moh. Abubakar