1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahmoud Abbas ya yi wa taron Majalisar Tarayyar Turai jawabi a birnin Straßburg.

YAHAYA AHMEDMay 16, 2006

Matsalolin da al'umman Falasɗinawa ke huskanta, sakamakon takunkumin da ƙasashen Yamma suka sanya wa Hukumar Hamas, sai ƙara taɓarɓarewa suke yi. Sabili da haka ne kuwa, shugaban Falasɗinawan da kansa, Mahmoud Abbas, yake ran gadin ƙasashen da ke da hannu a yunƙurin samad da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya, don neman shawo kansu su ci gaba da bai wa al'umman Falasɗinun taimako.

https://p.dw.com/p/Bu03
Mahmoud Abbas a Majalisar Tarayyar Turai, a birnin Straßburg.
Mahmoud Abbas a Majalisar Tarayyar Turai, a birnin Straßburg.Hoto: AP

’Yan majalisar tarayyar Turai da suka taru a birnin Straßburg, sun yi wa shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas kyakyawan tarbo. Amma duk da haka, jawabinsa na nuna cewa, ya zo ne a matsayin mai neman taimako ido rufe:-

„Ina tsaye yau gabanku ne da tabbacin cewa, ina yi wa ’yan majalisa jawabi, waɗanda da yawa daga cikinsu sun taɓa kai ziyara a Falasɗinu, kuma sun gano wa idanunsu, irin mummunan halin da al’umman Falasdinun ke ciki.“

Babu shakka, a cikin ’yan makwannin da suka gabata, wahalhalun da Falasɗinawan ke huskanta sun ƙara haɓaka. Tun da Ƙungiyar Haɗin Kan Turai, ta tsai da shawarar dakatad da biyan kuɗaɗe ga Hukumar Falasɗinwa, ƙarƙashin jagorancin Ƙungiyar islaman nan ta Hamas ne, aka sami giɓin Euro miliyan ɗari 5, a asusun hukumar. Hakan kuwa, ya sa hukumar ta kasa biyan ma’aikata dubu ɗari da 60 albashinsu, waɗanda suka haɗa da malaman makaranta, da jami’an tsaro, da likitoci, a Zirin Gaza da kuma Gaɓar Yamma, abin da ya sanya su cikin wani mawuyacin hali na ƙaƙa ni ka yi. Al’amura dai na ta kara taɓarbarewa ne a ko wace rana, a birane da ƙauyukan Falasɗinawan, inda a ko yaushe kuma, hauhawar tsamarin za ta iya janyo wani mummunan tashin hankali. A kann wannan batun ne Abbas ke yi wa ’yan majalisar tarayyar Turan gargaɗi, kuma da yawa daga cikinsu na sane da hakan.

Tun farkon wannan makon ne, Ƙungiyar Haɗin Kan Turai, da Majalisar Ɗinkin Duniya, da Amirka da Rasha suka bayyana shirinsu na cewa za su ɗan buɗe kan famfon kuɗi da zai turara zuwa yankin na Falasɗinawa. Rukunan guda 4 dai, kamar yadda ake yi musu laƙabi, sun ce za su fi ba da muhimmanci ne wajen kula da asibitoci da ayyukan kiwon lafiya. A birnin Straßburg, shugaban Falasɗinawan ya yi kira ga kaucewa daga yi wa Ƙungiyar islaman ta Hamas saniyar ware, duk da cewa, shi da kansa ma, a matsayin da ake kwatanta shi na mai sassaucin ra’ayin siyasa, na cikin masu sukar manofofin Hamas ɗin. Kamar dai ƙasashen Yamma, Mahmoud Abbas ɗin ma na bukatar Hamas ta guji duk wata gwagwarmaya da tashe-tashen hankulla, ta amince da wanzuwar Isra’ila tamkar ƙasa mai cin gashin kanta, sa’annan kuma ta yi amanna da duk yarjejeniyoyin da aka ƙulla da ƙasar bani Yahudun. Amma duk da haka, a birnin Straßburg, ya yi kira ga Majalisar Turan da ta bai wa hukumar Hamas ɗin damar balaga:-

„Sabuwar Hukumar na bukatar lokaci, don fahimtar irin sa ran da gamayyar ƙasa da ƙasa ke yi mata. Idan yanzu aka janye mata kuɗaɗe, wato kawai ana janyo hauhawar tsamari ke nan a ko’ina - wato a ma’aikatu da hukumomi - a Falasɗinun.“

Har ila yau dai, ƙasashen Yamman na yi wa Hamas ɗin ne kallon ’yan ta’adda. Sabili da haka, duk wani ɗan siyasan Turai ma na ɗari-ɗari wajen tuntuɓar ƙungiyar a hukumance.

Ita dai ƙungiyar Haɗin Kan Turai na neman hanyoyin ne, da za ta bi wajen tura wa Falasɗinawan kuɗi a Zirin Gaza da Gaɓar Yamma, ba tare da bi kan Ƙungiyar Hamas ɗin ba. To a nan ne kuwa har ila yau, ba ta san yadda za ta magance matsalar ba.