1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahawarar Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya

Mohammed, ZainabSeptember 25, 2008

Shekaru takwas bayan alkawari rage talauci nan da 2015

https://p.dw.com/p/FP8Z
Ban Ki Moon da Frank-Walter SteinmeierHoto: AP

Shugabannin gwamnatoci da ƙasashen duniya na cigaba da tursasawa bukatar daukar matakai tsaurara na cimma rage matsalolin talauci ,dauara da rikicin da kasuwannin hada-hada na kudi suka fada.

Dayake jawabi wa zauren Majalisar Ɗunkin Duniya a yau ,Babban Sakatare Ban Ki Moon ,yayi kira ga kasashen duniya dasu fito fili domin domin taimakawa shawo kan wannan matsala da duniya ke fama dasu.

Yace da isassun kudade da kuma manufa mai kyau daga bangaren gwamnatoci za a cimma nasarar shawo kan matsalolin talauci da yunwa da da cututtuka da ke addabar al'umma.

Shekaru takwas bayan da Wakilan majalisar suka dauki alkawarin cimma rage talauci da rabi nana da shekarata 2015,taron majalisar yana nazari tare da sanin irin matakan da zaa dauka na samun sauyi daga halin da ake ciki yanazu.

Ayayinda ake samun cigaba a wasu kasashe na duniya,babu kasa guda daga nahiyar Afrika data dauko hanyar cimma wani buri dangane da dukkan manufofin na MDD.

A farkon wannan makon nedai Ban Ki Moon ya sanar dacewar ,idan kasashe masu arziki zasu bada gudummowan kimanin kudi dala billion 72 a kowace shekara,zaa cimma nasarar yaki da talauci a duniya baki daya.

Yace halin da ake ciki na rikice rikicen kuɗi yana barazana wa rayukan billioyoyin mutane,daura da matsalolin tsadar abinci da hauhawar farashin mai.

To sai dai ministan harkokin wajen kasar Faransa Bernard Kouchner,ya bayyana shakku dangane da yiwuwar samun nasarar yaki da fatara a wannan yanayi da duniya take ciki.

Shi kuma Primiyan Britaniya Gordon Brown,kira yayi ga kasashe masu cigaban masana'antu da kada suyi amfani da wannan matsalar tattalin arziki da ake ciki yanzu ,wajen yin watsi da manufofin na Majalisar dunkin duniya.

Ayayinda shugaban Bankin Duniya Robert Zoellick,ya bayyana fargabarsa dangane da sakamakon rikicin kasuwannin hada-hada na kuɗaɗe akan ƙasashe masu tasowa da matalauta,wadanda tuni suke fama da matsalolin tsadar abinci da sauran kayan masarufi.