Mahawarar Majalisar Jamus kan manufofinta na ketare | Siyasa | DW | 24.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mahawarar Majalisar Jamus kan manufofinta na ketare

Jam'iyyun adawa sun soki manufofin Kasafin 2011

A yau ne  kasafin kuɗi na shekara ta 2011  na tarayyar Jamus ya shige matakai na biyu da na uku a gaban Majalisar Wakilai da ke a birnin Berlin.  Wannan dai yana mai zama al'ada ce inda akan  tabka mahawara dangane da manufofin gwamnati.

Mahawarar ta yau  dai ta kasance mai zafin gaske tsakanin gwamnati da 'yan Adawa da ke Majalisar Dokokin Jamus. Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta SPD Frank Walter-Steinmeier ya buɗe mahawara akan Kasafin kuɗi na 2011 ɗin da kakkausar suka ga gwamnatin haɗakar ta Angela Merkel. Ya ce ba a taɓa fuskantar matsaloli da ruɗani  da rashinda rtashin tsarin gwamnati kamar a wannan karon ba.

" Mene ne manufar wannan gwamnati, a ina ta tsaya, me take neman cimma buri, ina zata, wace irin manufa take dashi ga Al'umma. A kullun  sabon rikici da kalubalantar juna, tsakanin Brüderle da Röttgen, ko kuma tsakanin Westewelle da Guttenberg, kana a kullum Seehofer da dukkansu.  Waɗannan ƙananan rigingimu su na shafan harkokin siyasa, wanda yakan kawo wa jama'a takaici dangane da siyasa".

Renate Künast Fraktionsvorsitzende Neujahrsklausur

Renate Kuenast

Steinmeier dai ya zargi Angela Merkel da haifar da ruɗani tare da musgunawa wasu ƙasashe na Turai.

Sai dai shugabar gwamnati Merkel ta mayar da martani da zargin jam'iyyarsa ta  SPD da amince da karɓar Girka cikin ƙasashe masu amfani da takardar Euro tun a da farko, tare da rage ƙarfin dokokin daidata tattalin EU da ƙudurin kula da giɓin kasafin kuɗi, a lokacin gwamnatin Gerhard Schroeder.

Merkel ta zargi 'yan adawan da rashin yin amana da nuna halin kulawa da makomar ƙasar nan gaba, ballantana su rungumi zahirin halin da ake ciki.

" Ba ma yin ajiye domin nan gaba, sai dai wannan kasafin na nuni da cewar muna yin ajiya ne saboda nan gaba, wajen inganta kulawa da rayuwar Yara, harkokin ilimi da harkokin bincike domin inganta harkokin zuba jari. Waɗannan sune ababan dake kunshe a cikin kasafin kuɗinmu."

Shugabar gwamnatin Jamus ɗin dai ta yi kakkausar suka ga jami'iyyar masu akidar kare muhalli ta the Greens da cewar, inda ta zarge su da kin amincewa da cigaba tare da nuna adawa ga dukkan lamura.

" Hakan ba zai taɓa kasancewa ba. Da hakan ba zaku taɓa cin nasara ba, domin kunyi amana harkokin wasanni, amma idan ana wasannin Olympics a nan Jamus, su kuma ku nuna adawa da hakan".

Deutschland Bundestag Haushalt Frank-Walter Steinmeier

Frank Walter Steinmeier

Ita ma shugabar 'yan majalisar jami'iyyar FDP dake majalisar Birgit Homburger, ta bayyana jami'iyyar the Greens ɗin da kasancewa masu aƙidar naƙi, suna adawa da makamashin Nukiliya, da kwal da ma wayoyin lantarki.

Sai dai dukkan waɗannan kalamai na suka basu hana shugabar jami'iyyar The Greens ɗin Renate Künast yin martani ba.

" A takaice kasafin kuɗin naku gaba ɗaya shine: Manufofin gwamnatin haɗakar ba wani sabon abu bane wa ƙasar, ba a magance manyan ƙalubale da ake fuskanta a ɓangaren ƙwararru, kama daga bunkasa tattalin arziki, tsarin ilimi, sabunta makamashi. Makomar Ƙasar nan  na fuskanta barazanan. Har yanzu suna bin tsoffin  aƙida, a yayinda zamani ke jan mu. Kuma jamus ta cancanci makoma mai inganci"

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar Edita: Halima Balaraba Abbas

Sauti da bidiyo akan labarin