1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahawarar kasafin kudi a Bundestag

September 12, 2007

Ana ci gaba da mahawara akan kasafin kudin gwamnati a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag

https://p.dw.com/p/Btua
Bundestag
BundestagHoto: picture-alliance/ dpa

A lokacin mahawarar a majalisar dokoki ta Bundestag shugabar gwamnati Angela Merkel ta ce Jamus na da cikakken dalili na samun kwarin guiwa, domin kuwa tattalin arzikin kasar na bunkasa a yayinda a daya bangaren kuma ake samu raguwar yawam marasa aikin yi, kuma a karo na farko tun bayan sake hadewar kasar ana hangen daidaituwar al’amuran kasafin kudinta. Merkel ta kara da cewar:

“Wannan ba abin al’ajkabi ba ne. Hakan ya samu ne sakamakon aiki tukuru da kuma tu’ammali sau da kafa da gwamnati take yi da manufar garambawul din nan ta ajenda 2010.”

Wakilan jam’iyyar social-democrats dake hadin guiwa a gwamnati sun tafa wa shugabar gwamnati a game da wannan jawabi nata suna masu yin nuni da cewar wannan ajenda ta garambawul da tsofuwar gwamnati Gerhard schröder ta gabatar ita ce tushen nasarar gwamnatin dake ci a yanzun. Amma ‘yan hamayya sun danganta nasarar ce da wasu abubuwan dabam. ‘Yan jam’iyyar Freedemocrats, wadda ita ce tafi girma a tsakanin jam’iyyun hamayyar, sun danganta ci gaban da ake samu da farfadowar tattalin arzikin duniya. Wakilin jam’iyyar ta FDP Rainer Brüderle ya ce:

“Wajibi ne a yi amfani da bunkasar da ake samu a dangantakar tattalin arziki ta kasa da kasa domin kara aiwatar da garambawul da ya cancanta ga tsare-tsaren tattalin arziki na cikin gida. Amma abin mamaki sai ga shi ita gwamnati ta shiga wani hali na doki da murna tana mai bin wasu manufofi na iya yi tare da almubazzaranci.”

Bisa ga ra’ayin jami’in siyasar na Freedemocrats wajibi ne gwamnati tayi sassaucin haraji ta yadda jama’a zasu ci gajiyar bunkasar tattalin arzikin da ake samu. Ita ma jam’iyyar hadin guiwar ‘yan gurguzu sai da tayi korafin cewar ma’aikata basa cin gajiyar bunkasar tattalin arzikin. Kakakinta a majalisar dokoki Oskar Lafontaine yayi tofin Allah tsine akan abin da ya kira rashin motsin albashi da kuma dardar da mutane ke ciki game da makomar guraben ayyukansu. Lafontaine ya kara da cewar:

“Abin dake akwai shi ne kasancewar mutane sai dada shiga hali na kaka-nika-yi suke game da makomar rayuwarsu a nan kasar ta Jamus sakamakon matakan da gwamnati ke dauka na tsawwala harajin kayan masarufi, a yayinda a daya bangaren take wa ‘yan kasuwa sassaucin haraji.”

Sai dai kuma shugabar gwamnati Angela Merkel ta ce maganar sassaucin harajin bata taso ba. Ta ce ba zata iya yi wa mutane alkawarin da ba zata iya cikawa ba, musamman ma ganin cewar akwai jan aiki a gaban gwamnatin hadin guiwar a shekaru biyxun da suka rage na mulkinta.