Mahawara tsakannin Obama da McCain | Siyasa | DW | 08.10.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mahawara tsakannin Obama da McCain

Alkalumma sun nuna cewar a karo na biyu, Obama na jam'iyyar Demokrat ya sake samun galaba McCain na jam´iyar Republican

default

McCain da Obama

Mahawarar wadda a wannan karo aka yi ta a jami'ar Belmount dake birnin Nashville, Barack Obama wanda a da ake gannin ke da jan aiki a gabansa idan har yana da burin samun ƙuri'un mafi yawan fararen fata na Amirka, ya hau kujerarsa cikin wani hali na kwanciyar hankali da sannin abin da ya kawo shi. Muhimmin batun da ya fi ɗaukar hankali a wajen mahawarar shi ne maganar faɗi tashi da bankunan Amirka ke fama da shi wanda ke barazana kan tattalin arzikin ƙasar. Obama ya ce shirin agaji na dala miliyan dubu ɗari bakwai da gwamnatin Amirka ta gabatar wani mataki ne na farko wajen magance wannan matsala. Obama ya ƙara da cewa:

"Masu matsakaicin ƙarfi ma na buƙatar wani shiri na ceto wanda ke da nufin rage yawan haraji, taimako ga masu mallakar gidaje don su cigaba da mallakar gidajensu. Kuma a nan yana nufin cewar mu ƙara yawan kuɗaɗen da aka ware na inganta harkokin rayuwa, da suka haɗa da kyakyawan tsarin inshora na kiwon lafiya, samar da aikin yi ga al'uma tare da kyautata hanyoyin sadarwa da ababen jin daɗin rayuwa."

Ko abokin hamayyarsa John McCain ya yi amanna cewar wajibi ne a taimakawa masu matsakaicin ƙarfi wajen rage harajin gidaje don bawa al'uma wata kariya a game da gidajensu. Sai dai a yayin da Barack Obama ke kira da a ƙara yawan haraji na masu kuɗi, shi kuwa McCain nema yake a bar haraji ta bai ɗaya .

"Bana goyan bayan ƙara yawan harajin da masu kuɗi ke biya, haka kuma bana goyan bayan sake fasalin tsarin biyan haraji, ya kamata a bar yawan kuɗaɗen harajin kamar yadda suke a yanzu haka."

Ra'ayoyin 'yan takaran biyu suna cigaba da saɓawa juna a bangarori da suka shafi inshora kan kiwon lafiya, inda Obama ke da imannin cewa wannan wani haƙi ne na jama'a, McCain ya musanta haka.

A ɓangaren makamashi kuwa, John McCain ya fi son a faɗaɗa shi. Haka kuma a harkokin diplomasiya, McCain yace yana da cikakkiyar masaniya a inda ake buƙatar taimako daga Amirka.

"Ina cike da imani cewar rashin bada goyan baya kan tsugunar da mayaƙan ruwan Amirka a ƙasar Libanon tare da goyan bayan da na bayar wajen tura jami'an tsaro zuwa ƙasashen Kosovo, Bosnia tare da yaƙin yankin Gulf na farko sun nuna irin zurfin ƙwarewa da nike da shi a fannin harkokin diplomasiya."

McCain ya soki Obama da cewar ya tabka kurakurai a batun ƙara yawan jami'an tsaro a Iraqi haka kuma a game da batun mamayar Jojiya da Rasha ta yi.

A lokacin da yake amsa tambayoyi a game da rikicin yankin gabas ta tsakiya kuwa, McCain cewa yayi ba zai ma jira amincewar majalisar datawan ƙasar kafin ya ɗauki matakin tura jami'ai zuwa ƙasar Izraila ba idan har ta buƙaci taimakon Amirka. A amsa wannan tambaya, Barack Obama ya nuna cewar zai nemi goyan baya daga sauran ƙasashen duniya wajen shawon kan Iran ta martaba dokoki dake tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Bayan wannan mahawara dai ra'ayoyin jama'a da gidan telebijin na CNN ya tattara ya baiwa Obama kashi 54 cikin ɗari na ƙuri'u a yayin da McCain ya samu kashi 34. 'Yan takaran biyu zasu sake karawa a mahawara ta ƙarshe a ranar 15 ga wannan watan da muke ciki a Hempstead dake birnin New York.