Mahawara kan Musulunci tsakanin Jamus da Turkiyya | Siyasa | DW | 29.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mahawara kan Musulunci tsakanin Jamus da Turkiyya

Babban taron jam'iyyar AFD da ke Jamus da ake zargi da kyamar Musulunci zai fayyace dangantaka da addinin Islama a kasar da koyarwar limaman Turkiyya

Wani masallaci a birnin Köln

Musulmi a wani masallacin birnin Köln na Jamus

Tattaunawa mai sarkakiya da ake yi da kasar Turkiyya yanzu ta koma kan batun addini, inda ake saka ayar tambaya kan abubuan da limaman baki 'yan kasashen ketare da ba su da masaniya kan rayuwar yau da kullum ta Jamusawa, ke koyarwa a masallatun kasar ta Jamus. Hakan dai na zuwa ne yayin da a karshen mako jam'iyyar nan ta AFD da ake zargi da kyamar Musulunci za ta gudanar da babban taronta, da jadawalinsa zai fayyace yadda za a yi dangantaka da addinin Islama a Jamus.

Ko da yake daga baya shugaban Turkiyya Recep Tayip Erdogan ya ce kasarsa ba ruwanta da bin wani addini, amma kalaman da Shugaban Majalisar Dokokin Turkiyya Ismail Kahraman ya yi a karshen mako cewa Turkiyya kasar Musulmi ce da ya zama wajibi a sama mata kundin tsarin mulki na shari'ar Musulunci, ya sake tayar da mahawara a Jamus na irin rawar da Limaman Turkiyya ke takawa a masallatan Jamus. Ta kan kungiyar Musulmin Turkiyya a Jamus wato Ditib, limamai kimanin 970 daga Turkiyya suke limanci a Jamus.

Jamusawa na zargin gwamnatin Turkiyya da kokarin fakewa da kungiyar ta Ditib da kuma limaman don yada manufofinta na siyasa a Jamus. Shin kuwa haka ne Turkiyya na amfani da masallatan a Jamus don cimma manufofinta? Hamideh Mohagheghi 'yar kimiyyar addini a jami'ar Paderborn ta ce a aikace masallatan Jamus ba su da zabi face su dauko limamai daga ketare.

Hamideh Mohagheghi wissenschaftliche Mitarbeiterin Universität Paderborn

Hamideh Mohagheghi 'yar kimiyyar addini a jami'ar Paderborn

"Kawo yanzu ba a horas da limamai a Jamus. Cibiyoyin da muke da su, inda yanzu ake horas da limaman sabbi ne da ba su kai ga yaye limamai ba. Saboda haka ake dauko limamai daga ketare."

Dokokin Jamus ma dai na tarnaki ga samun sauyi a halin da ake ciki. Dokar kasar dai ta ba wa kowace gamaiya ta addini ciki har da Musulunci, cikakken 'yancin tafiyar da aikinta ba tare da nuna bambamci tsakani ba. Mouhanad Khorchide shugaban cibiyar nazarin addinin Musulunci a jami'ar birnin Münster ya ce bai ga wani abu mai ta da hankali da ya saba wa kundin tsarin mulkin Jamus daga limaman da kungiyar Turkawan Jamus ta Ditib ke shigo da su kasar ba, to sai dai yana da wata damuwa guda daya.

"A matsayin masanin addini, damuwa ta daban ce, wato akasarin limaman ba su iya Jamusanci ba, ba su da masaniyar ainihin rayuwar matasa a Jamus. Ba su waye da yanayin rayuwar da matasa Musulmi a Jamus ke ciki ba. Saboda haka ba sa iya zama wadanda matasan za su iya tuntuba a kan batun addini ba".

Masanin ya ce sau da yawa matasan ba sa sha'awar zuwa masallaci domin hudubar da limaman ke yi sun sha bambam da yanayin rayuwa a Jamus. Saboda ya goyi bayan horas da limamai a Jamus.

Mouhanad Khorchide Islam Wissenschaftler Uni Münster

Mouhanad Khorchide shugaban cibiyar nazarin addinin Musulunci a jami'ar birnin Münster

"Ina goyon bayan horas da limamai a Jamus wadanda suka san yanayin zamantakewar kasar da za su iya danganta shi da addini, amma ba wadanda za su saka matasan cikin tunanin yin zabi tsakanin Musulunci da zama Bajamushe ba. Amma limaman da za su karfafa guiwar matasan buga kirji da zaman Musulmi kuma Jamusawa."

A wannan alkiba ake kokarin tafiyar da Musluncin a Jamus in ji Hamideh Mohagheghi masaniyar addinin Muslunci.

"Kowane addini na tafiya da zamani da kuma al'adun al'ummar da ke bin addinin. Al'ada da rayuwar yau da kullum na da tasiri kan addini. Saboda haka yake da muhimmanci a daidaita koyarwar addinin Muslunci da rayuwar al'ummar Jamusawa."

Masanan dai na masu kyautata fatan cewa za a cigaba da kokarin sabunta koyarwar addinin ta yadda za ta dace da sauyin rayuwa ta yau da gobe.