Mahawara kan Dan Tarzoma | Labarai | DW | 06.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahawara kan Dan Tarzoma

Shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel tayi kira ga membobin jamiiyyar ta na masu raayin rikau watau CDU,dasu dada nuna hakuri dangane da irin suka da suke yi dangane da mataki da zaa dauka kann Dan tarzoman kasar da aka yankewa hukunci.

Shugaba Horst Köhler,wanda ya gana da Christian Klar na tsohuwar kungiyar tarzoma ta Red Army a ranar hjumaar data gabata,anasaran cewa,a wannan makon ne zai sanar da ko zaa sallami Mr Klar daga gidan yari kafin karewan waadinsa.Yana dai tsare a kurkuku ne tun shekaru 24 da suka gabata ,adangane da irin rawa daya take cikin kisan gilla da akayi a baya.Wasu yan jammiiyyar masu raayin rikau din dau,na masu raayin cewa a bar Mr Klar ya cigaba da zama gidan wakafi,saboda bai nuna alamun nadama ko kadan a dangane da laifuffukansa ba.