Mahawara dangane da sajewar Baƙi da barazanar Tarzoma | Zamantakewa | DW | 25.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Mahawara dangane da sajewar Baƙi da barazanar Tarzoma

Halin da musulmi ke ciki a tarayyar Jamus sakamakon barazanar 'yan Tarzoma

default

Thomas de Maiziere

'Yan Siyasa na ci gaba da tofa kamalaman sukar Baƙi musulmi na rashin sajewa cikin al'ummar Jamusawa, adaidai lokacin da mahawara ke daɗa zafafa dangane  da irin barazanar da ke tattare da sajewar Baƙi a nan Jamus.

A farkon wannan makon ne dai ministan harkokin cikin gida na Jamus Thomas de Maiziere, ya yi gargaɗi dangane da bukatar dainaa zargin Musulmi kan barazanar da ƙasar ke fuskanta dangane da kai mata harin ta'addanci  ba tare da wata  hujja ba.

A taron daya gudanar da gammayyar 'Yan anda, Minisatn ya bayyana cewar gwamnati ba zata naɗe hannunta ta na kallo ana nunawa al'ummar musulmi kiyayya ba, sakamakon barazanar 'yan tarzoma, ba tare da ɗaukar mataki ba.

De Maiziere ya ce kada mu yi amfani da mahawarar dake gudana a yanzu wajen zargin musulmi masu bin doka da Oda a cikin ƙasar. A cewarsa 'Yan tarzomar nada nufin tsoratar da mutane ne, tare da gargaɗi dangane haifar da wata kiyayya da zata haifar da matsala.

Nadeem  Elyas Wakili ne a majalisar tuntuɓar juna ta musulinci ta kasa anan tarayyar Jamus wanda a cewarsa sakamakon wannan yanayi al'ummar musulmi na cikin hali mawu yaci ta fannoni biyu anan Jamus, wanda ya ce

Gläubige Bosnische Islamische Kulturgemeinschaft Gazi Husrevbeg Köln Archiv 2010

"  da farko ana ɗora mana dukkan nau'i  na  azabtarwa kamar yadda akewa waɗanda ba musulmi a anan kasar. Na biyu kuma muna fama da wannan babban zargi da ake mana dangane da barazanar ayyukan tarzoma, hakan yana mana zafi, ko da kuwa ba haka manufar 'yan siyasa take ba".

Adangane da cigaban barazanar kai hare-haren ta'addanci a nan tarayyar Jamus kuwa Nadeem  Elyas cewa yayi...

" Muna fuskantar  ninkin matsaloli dangane da wannan hali da ake ciki, kuma muna fatan cewar waɗannan mutane zasu kasance masu sanin ya kamata, tare da samarwa da ƙasarmu ta al'ummarta kariyar data dace"

 A yanzu haka dai al'ummar Musulmi wajen miliyan huɗu da su ke zaune a nan Jamus da suka kama daga Larabawa, Turkawa, 'yan Afganistan da ma wasu Jamusawa da suka musulunta, da sauransu, wasu ma da takardun shaidar kasancewa 'yan asalin ƙasar, na fuskantar matsalolin da basu da masaniya akai daga 'yan siyasa da ma kafafun yaɗa labaru.

Babban editan  mujallar Stern dake fitowa mako-mako Andreas Petzold, ya bayyana cewar mahawara dangane da rayuwar musulmi anan tarayyar Jamus yana ɗaukar wani salo. Ya ce abun takaici ne wannan mahawar da ke cigaba da gudana dangane da sajewar baƙi, kuma daka karshe a mayar da hankali kacokan kan musulmi.

Axel Koehler und Nadeem Elyas mit Aiman A. Mazyek

Nadeem Elyas da wasu Jami'ai

Ko yaya rashin goyon  baya ga musulmi yake a ɓangaren gwamnati. Nadeem Elyas na majalisar Tuntuɓar juna ta musulunci ta Jamus yana mai cewar..

" mun sha kokawa dangane da wannan gazawar wannan goyon bayan, ba wai kawai saboda harin da aka kaiwa Masallacin Berlin ba, amma saboda Al'ummar muslmi sun dade da kasancewa cikin wannan halina ƙuncin rayuwa, sakamakon aika-aikan masu ra'ayin tsananin kishin addini. Muna sane da hakan a masallatanmu, kazalika a tsakanin matanmu da yarammu.Muna fama da rashin goyon baya. Haka zalika muna karancin  rashin ɗaukar matakai a siyasance , na ceto wannan adadi na na musulmi da ke zaune anan Jamus kimanin miliyan 4.3 daga hanasu gudanar da rayuwarsu cikin 'yanci".

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita          : Mohammad Nasir Awal