1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahawara a zauren taron Davos

Zainab MohammedJanuary 30, 2009

Matsalolin tattalin Ariki da yadda zasu shafi ƙasashe masu tasowa

https://p.dw.com/p/GkDq
SwitzerlandHoto: AP

Ayayin da Duniya ke kokarin kalubalantar matsalar tattalin arziki da ake ciki, yawancin ƙasashen yammaci na Turai suna da saɓanin martani dangane da ɗumbin kuɗaɗen da ake cigaba da gabatarwa domin ceto masana'antun kuɗade, da ɗaukar nauyin Bankuna.To sai dai ko wane hali ƙasashe matalauta da masu tasowa ke ci? Wannan na ɗaya daga cikin batutuwa da taron nazarin makomar Al'umma a birnin Davos ke tattaunawa.

Da farko lokacin da matsalar tattalin arzikin ta fara yaɗuwa daga kasa zuwa wata kasa dai, akwai kyakkyawar fatan a wasu bangarorin na cewar watakila ƙasashe matalauta bazasu ji raɗaɗin matsalar sosai ba.

A 'yan shekarun da suka gabata dai ƙasashe masu tasowa da dama sun fuskanci matsakaicin ingantuwan tattalin arziki. Amma kasancewa mafi yawan ƙasashe masu tasowan basa taka wata muhimmiyyar rawa a harkokin tattalin arzikin ɗuniya, kusan za a iya cewar basa fuskantar barazanar halin da ake ciki a kasuwannin hada-hada na kuɗaɗe, kamar takwarorinsu masu tasowa.To ko me zai hana su tsira a yanzu?

Erdogan in Davos
Hoto: picture-alliance/ dpa

Shugaban ɗaya daga cikin masana'antun kudi na Asia,da ake kira Morgan Stanley Asia, watau Stephen Roach, yana mai ra'ayin cewar hakan nada nasaba da tsintan kanta da Duniya tayi cikin hali mawuyaci a tarihi na tattalin arziki...

"Wannan shine karon farko tun bayan yakin duniya na biyu,da da aka fuskanci matsaloli dangane da kayyayakin da ake sarrafawa a duniya baki daya.Wannan kuwa nada nasaba ne da irin halin koma bayan tattalin arziki da kasashe masu arzikin masana'antu suke fuskanta.Wannan kuma ya tarwatsa fatan kasashe masu tasowa wadanda ke ganin damar samun riba idan suka shigar da kayayyakin da suka sarrafa kasuwannin duniya.Dukkannin ƙasashe masu cigaban masana'antu na cikin hali mawuyaci na tattali"

Shima ministan harkokin kuɗi na kasar Afrika ta kudu Trevor Manuel yana da wannan ra'ayi...

"Ina ganin wannan matsala ce ta gajeren lokaci ga Afrika,yanayi ne mawuyaci,dole mu jure fuskantarsa shi"

Erdogan in Davos
Recep Tayyip ErdoganHoto: AP

Wani sabon tsari da cibiyar nazarin harkokin kudi tayi ,ya bayyana irin hali mawuyaci da kasashe matalauta zasu kasance.Inda yake nuni dacewar za a samu raguwan yawan kudaden dake zuwa kasashe masu tasowa daga hannun mutane da wajen kashi 2 daga cikin 3,kwatankwacin dala biliyan 165 kenan a shekarara,daga biliyan 466 kamar yadda aka saba.Batu da ministan kudin na Afrika ta kudu Manuel ya hakikance...

"Na san cewar muna ganin janyewar wasu daga cikin ayyuka.A janhuriyar Demokradiyyar Kongo,akwai ayyukan hakan ma'adinai kimanin 48 akayi watsi dasu a matakai daban daban"

Mafi yawa daga cikin daga cikin gwamnatocin kasashen yamma zasu mayar da martani ta hanyar ɗaukar nauyin kamfanin da suke ganin yana da matukar muhimmanci a harkokin tattalin arzikinsu.

Sai dai Shugaban Kamfanin gudanar da ayyukan gyaran hanyoyin gwamnati a Afrika ta kudu ta Transnet, Mario Ramos, hakan ba makoma mai kyau bane wa ƙasashe masu tasowa..

"Abun takaicin shine, duk dacewar ƙasashe masu cigaban masana'antu zasu iya bayar da dumbin kuɗaɗe domin ceto masana'antun kudadensu,ƙasashe masu tasowa da matalauta basu da sukunin da zasu iya bayar da irin wadannan kuɗaɗe domin ceton nasu masana'antun"

Weltwirtschaftsforum Davos Wen Jiabao
Wen JiabaoHoto: AP

Bugu da kari inji Ramos akwai ninkin matsayi tsakanin kasashe masu cigaban masana'antu da masu tasowa....

"Wasu daga cikin matakai da yanzu ƙasashe masu cigaba ke amfani dasu da kuma tsarin da suke aiwatarwa, batutuwa ne da hukumar bada lamuni ta majalisar Ɗunkin Duniya watau IMF da Bankin duniya suka haramta wa kasashe masu tasowa aiwatarwa"


Ayayinda kwararru da dama suka amince da nazarin halin da ake ciki,da kuma makomar duniya nan gaba, musamman kasashe masu tasowa, har yanzu baa samar da shukunin shawo kan matsalolin ba. Sai a kullun aka fara mahawara akan ambaci tsarin hadin kai tsakanin kasashe domin shawo kan matsalolin.Trevor Manuel yace hakan ne zai iyataimaka wajen kare matsaloli makamantan haka nan gaba...

"A ganina daya daga cikin gazawar da aka fuskanta a shekarun baya,shine rashin tunkarar matsaloli a matsayin kasashe masu yawa.A maimakon haka akan ajiye kasa a matsayin mai karɓan rance ,ko kuma mai bayarwa.A maimakon abokan hulɗoɗi.Ya zamanto wajibi a sauya wannan tsarin."