1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An buɗa gidan abinci Halal a Faransa

April 21, 2010

Mahawwara game da buɗe gidan abinci Halal zalla a birin Roubaix na ƙasar Faransa domin mabiya addinin Islama.

https://p.dw.com/p/N2Lf
Gidan "Quick" na abincin Halal a RoubaixHoto: AP

Kwanakin baya an tafka mahauwra akan wani gidan cin abinci mai suna "Quick" bayan da ya ɓullo da wasu sabin gidajen cin abinci na Halal.

A cikin ƙasashen Turai ƙasar Faransa ke sahun gaba wajen yawan musulmi.

Ƙiddidiga ta nunar da cewa, musulmi a Faransa sun kai aƙalla miliyan shidda.

Mafi yawan su sunje tun lokacin mulkin mallaka daga yankin Magreb da kuma wasu ƙasashen Afrika da suka haɗa da Mali, Senegal, Guinée dadai sauransu.

Da dama sun ayyayafa kuma sun riƙe addini da ɗabi´o´in musulunci.

Ta la´akari da yadda musulmin ke cigaba da ƙara bunƙasa a Faransa yasa wani kamfanin gidan abinci mai suna "Quick" ya yanke shawara girka wani shago na saida kayan abincin Halal zalla, wato abinci da bashi da garwaye da duk wani abun da cin shi ko kuma shan sa, ya saɓawa dokokin addinin musulunci.

An kafa wannan shago a Roubaix ɗaya cikin biranen Faransa, daya ƙunshi musulmi masu tarin yawa.

Roubaix dake yankin arewancin Faransa kusa da iyaka da ƙasar Beljiam na da kamfanoni da masana´antu masu yawa, saboda haka yayi suna ta fannin karɓar baƙi.

Tun shekara 1960 ma´aikaci musulmi na farko daga yankin Maghreb ya fara aiki a birnin Roubaix.A yanzu birnin ya ƙunshi dubunan jama´a musulmi ´yan asulin ƙasashen Tunisiya, Aljeriya da Marroko.

Malik wani matashi ne musulmi dake Roubaix, yana zaune a gidan abinci "Quick" da bredinsa shaƙe da naman rago cikin hannunsa, ya bayyana farin ciki game da yadda a yanzu aka buɗa gidan abinci inda zai iya samun nama halal tsantsa:

Abu ne mai kyau, ko ba komai rayuwa ta ƙara ingantuwa a Roubaix, saidai muna fata cuɗe ni in cuɗe ka ta ƙara faɗaɗa.

A ƙasar Faransa kamfanin abincin "Quick" na da rassa fiye da 360.

A halin yanzu takwas rak daga cikin su ke sayar da abincin Halal zalla.

A cikin wannan shaguna babu giya da duk wasu kaya masu sa maye, ba a saida naman aladai, ko kayan masarufin masu gauraye da naman aladai.Sannan akwai hajoji iri-iri dukansu masu lambar Halal wanda suka haɗa da Coca-Cola, kayan wasa na ƙananan yara, da kayan tanɗe-tanɗe da lashe-lashe.

To saidai wannan mataki ya jawo mahaura mai zafi a fagen siyasar Faransa, mussamman lokacin yaƙin neman zaɓen jihohi a watan da ya gabata.

Jam´iyar FN ce, mai ƙyamar baƙi ta Jean Marie Lepen ta fara yin Allah wadai da al´amarin.

Amma a ra´ayin Abil wani musulmi dake Roubaix ƙirƙiro shagon Halal bai zama lefi ba:

Idan mafi yawan masu sayyaya a shagon na buƙatar samun nama na halal daidai ne gidan abinci "Quick" ya saida abunda mafi yawan jama´a suka fi buƙata.

Ga musulmin dake zaune a Roubaix samun gidan abinci Halal na matsayin babban cigaba, domin a yanzu saɓanin kwanakin baya, zasu iya cin nama, wanda aka yanka tare da yin amfani da ƙa´idojin addinin islama, to saidai a yayin da yake bayyani akai, magajin garin Roubaix René Vandierendonck ya bayyana adawa da keɓe shago na mussamman ga mabiya wani addini, a game da haka ya shigar da ƙara kotu:

Ya kamata ayi takatsantsan, domin wannan mataki za a iya danganta shi da wariya.Kuma hakan ba zai kyau ba,ga dukan jama´ata, wanda ba musulmi da musulmin.

Saidai daga bisani magajin garin ya janye ƙarar da ya shigar, bayan ya tattana da hukumomin "Quick", wanda suka ce zasu ɓullo da wata hanya ta yadda kowa zai sami biyan buƙata.

Itama Marine Lepen ɗiyar Jean Marie Le Pen shugaban masu ƙyamar baƙi a ƙasar Faransa ta bayyana aniyarta ta yaƙar matakin buɗa shagunan abincin Halal a Faransa:

Nan ina ´yancin sauran jama´a ? Ina ´yancin masu bin wani addini daban, da wanda basu da addini gaba ɗaya ?.

A yayin da yake tsokaci game da wannan mahaura shugaban jam´iyar masu radin kare mahhali Daniel Cohn-Bendit cewa yayi bai damu da batun wani gidan abinci ya sayar da abinci halak ko haram ga wani addini, abinda ya dame shi,shine ko wane shagon abinci ya maida hankali wajen sayar da abincin da aka samu ta hanyar noma sak, ba wai noma ba ta hanyar yin amfani da sinadarai irin na zamani, masu gurɓata yanayin ɗan adam.

Mahaura game da wannan shago mai saida kayan Halal zalla ta ɗauki saban salo a ƙasar Faransa , domin ta rikiɗa zuwa mahaurar siyasa.

Philippes Le Breton na jam´iyar PS shima na daga masu ra´ayin cewar ware shago na mabiya wani addini zalla zai raunana dokar ´yancin addini a Faransa:

Ta la´akari da mahaurar da aka tafka game da batun niƙabi, da kuma yadda nike sauraran iyayen yara su na kira domin samar da abincin Halal ga yaransu a cikin makarantu.Zan iya cewar an gurgunta dokar da ta tanadi cewar, Faransa ƙasa ce inda aka raba siyasa da addini, kuma wannan doka ce mai mahimmanci.

To raba addini da siyasa, kokuma gauraye su wuri guda, a ƙasar Faransa dai shagunan Halal sun sami karɓuwa matuƙa daga muslumi.

Alƙalluman da wata cibiyar bincike mai suna Solis ta gudanar sunyi hasashen cewar ,a shekara ta 2010 za a sami cinaki na zunzurutun kuɗi wuri na gugar wuri, har Euro miliyan dubu biyar da rabi na kayan Halal.A shekaru biyar da suka gabata, alƙalluman sun ce addadin cinikin ya tashi miliyan dubu ukku.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Mohamed Nasiru Awal