Mahaura a majalisar dattawan Amurika a game da yaƙin Irak | Labarai | DW | 12.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahaura a majalisar dattawan Amurika a game da yaƙin Irak

Yan majalisar dattawan Amurika sun cimma daidaito, a game da wajibcin gudanar da ksawkwasrima ga tafiyar da al´amuran yaƙin ƙasar Irak.

To saidai saɓanin yadda yan majalisar Demokrate su ka bukata, ba a samu nasara cimma rinjaye ba, a game da janyewar sojojin Amurika kwata-kwata kuma cikin gaggawa daga ƙasar.

Yar takara a zaɓen shugaban ƙasa Amurika, bugu da ƙati yan majalisa Hillary Clinton, ta bayyana buƙatar ragewa shugaba Bush ƙarfin iko, a game da wannan rikici, ta hanyar gudanar da wasu cenje-cenje ga dokokin Amurika.

A ɗaya wajen kuma ,ƙungiyoyin daban daban sun gabatar da shawawari wanda, dukkan su,su ka tattatru akan mahaɗa guda,wato kawo ƙarshen yaƙin Irak.

To saidai har ya zuwa yanzu, shugaba Georges Bush na Amurika, ya yi tsawuwar gwamen jaki ,a game da buƙatar sa, ta sai ya tsarkake wannan ƙasa daga gurbattatun yan ta´ada.

Rikicin Irak ya hadasa matuƙar baƙin jinni ga shugaba Bush a ciki da wajen Amurika.