Mahaura a Majalisar Ɗinkin Dunia | Labarai | DW | 22.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahaura a Majalisar Ɗinkin Dunia

A na ci gaba da tabka mahaurori a birnin New York na ƙasar Amurika,albarkacin taron shekara –shekara, na shugabanin ƙasashen MDD karo na 61.

A ranar jiya, jawaban da su ka fi ɗaukar hankulla, sun haɗa da na shugaban ƙasar Libanon, Emil Lahud, da na shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas.

A jawabin da yayi, Lahoud ya bayyana matuƙar takaici, a game da halin ko in kulla, da Majalisar Dinkin Dunia ta nuna, da farkon yaƙin da a ka gwabaza kwanakin baya, tsakanin dakarun Isra´ila ,da na Hizbulahi, wanda a sakamakon sa bani yahudu, su ka yi kaca -kaca da Libanon.

Shi kuwa shugaban hukumar Palestinawa, ya tabatar da girka gwammnatin haɗin kan ƙasa a Palestinu, da za ta ƙunshi ƙungiyoyin Fatah da na Hamas, kazalika, ya ce wannan gwamnati, da zaran an girka ta, za ta amincewa da Isra´ila, a matsayin ƙasa mai cikkaken yanci.

A ɗaya hanun kuma, shugaban ƙasar Venezuela Hugo Chavez, ya ƙara caɓo ta.

Bayan jawabin da yayi, wanda a cikin sa, ya danganta Georges Bush, na Amurika da tantirin sheɗani,jiya kuma cewa yi, Georges Bush cikkaken ɗan ƙwaya ne, ƙarewa da ƙarau, shugaban Venezuela, yace, Bush ba zai rasa taɓuwar hankali ba.

Ya yi wannan jawabi, a lokacin da ya kai ziyara, a Harlem cikin New York.