Mahaura ƙeƙe -da ƙeƙe tsakanin N. Sarkozy da S. Royal | Labarai | DW | 03.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahaura ƙeƙe -da ƙeƙe tsakanin N. Sarkozy da S. Royal

A daren jiya, a ƙasar France a ka gwabza mahaura farko ta ƙeƙe da ƙeƙe tsakanin yan takara 2 a zaɓen shugaban ƙasar France, zagaye na 2,wato Nikolas Sarkozy na jam´ miyar UMP mai riƙe da ragamar mulki da kuma Segolene Royal, ta jama´iyar PS mai adawa.

A tsawan kussan sa´o´i 3, yan takara sun bayyana burin su, ga ƙasar France idan su ka ci zaɓe.

Wannan mahaura ta ɗau zafi, a lokacin batutu wanda su ka shafi al´amuran makarantu, inda yan takara 2 su ka samu banbacin ra´ayi mai yawa.

Yan sa´ao´in ƙalilan bayan wannan mahaura, ɗan takara da ya zo na 3, a zagayen farko, wato Fransois Bayrou, ya tabbatar da cewa, ba za shi zaɓen Nikola Sarkozy ba, a zagaye na 2.

Saidai a ra´ayin mafi yawan al´umommin ƙasar France an yi mutuwar kasko a wannan mahaura.

Suma kafofin da ke ƙiddididar jin ra´ yin jama´a, sun jaddada matsayin da yan takara 2 ke ciki ,kamin gudanar da mahaurar ta jiya, wato har yanzu, Nikolas Sarkozy a ke kyautata zaton zai lashe zaɓen na ranar lahadi mai zuwa tare da kashi 52 bisa 100 ,na yawan ƙuri´un da za a kaɗawa.