Mahaukaciyar guguwar Wilma ta ratsa yankin tsibirin Yucatan na Mexiko | Labarai | DW | 22.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahaukaciyar guguwar Wilma ta ratsa yankin tsibirin Yucatan na Mexiko

default

Hade da ruwan sama kamar da bakin kwarya da kuma wata iska dake gudun sama da kilomita 220 cikin awa daya, mahaukaciyar guguwar Wilma ta ratsa yankin tsibirin Yucatan dake Mexiko. Guguwar ta yi awan gaba da bishiyoyi da palwaya da kuma rufin gidaje. Rahotanni sun ce mutane da dama sun samu rauni to sai dai ba wanda ya rasa ransa kawo yanzu. A wani mataki na rigakafi an kwashe dubban mutane ciki har da ´yan yawan shakatawa da yawa zuwa tudun mun tsira. Masu hasashen yanayi sun ce bayan ta ratsa yankin tsibirin na Yucatan, guguwar ta Wilma zata doshi jihar Florida ta Amirka bayan ta danna da yammacin kasar Cuba. Cibiyar nazarin mahaukaciyar guguwa a birnin Miami ta yi gargadi game da aukuwar wani mummunan bala´i.