Mahaukaciyar guguwar Sidr a ta kashe sama da mutane 2,600 | Labarai | DW | 19.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahaukaciyar guguwar Sidr a ta kashe sama da mutane 2,600

Kwanaki huɗu bayan mahaukaciyar guguwar nan ta Sidr data ritsa da kasar Bangldash daya kashe kusan mutane 2,600,jami’an agaji na kokarin isa yankuna dake gaɓar koguna dake wajen gari,domin tallafawa miliyoyin mutane da suka tsira da rayukansu.Jami’an raba kayan agajin dai sun bayyana irin matsanancin wahala da suke fuskanta,a ƙokarinsu na isa cikin tsaunuka domin tallafawa waɗanda suke wannan yanki na Bagerhat,inda nan ne guguwar tafi yin ɓarna.Shugaban ƙungiyar agajin kasa da kasa ta Red Cross dake Banghladash Mohammed Abdur Rob,yace a yanzu haka sama da mutane 3,000.suka rasa rayukansu,kuma adadin zai iya karuwa.Sai dai yace suna fuskantar barazanr yankewan abinci da ruwa da magunguna wa mabukata,wanda hakan zai iya haddasa ɓarkewar cututtuka.