1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahaukaciyar guguwa ta Wilma ta doshi kudancin nahiyar Amirka

October 20, 2005
https://p.dw.com/p/BvOd

Hukumomi a kasashen Mexiko da Cuba sun fara kwashe jama´a zuwa tudun mun tsira a daidai lokacin da mahaukaciyar guguwar Wilma ke kara dannawa a yankin kudancin Amirka. Kuba ta ba da umarnin kwashe mutane kimanin dubu 235 daga lardin Pinar del Rio dake yammacin kasar. Sannan a yankin shakatawa na Cancun dake Mexiko hukumomi sun yi kira da ´yan yawon bude ido su kimamin dubu 30 da su hanzarta tattara nasu ya nasu su fice daga yankin tsibirin Yukatan. Masu hasashen yanayi sun ce a gobe juma´a mahaukaciyar guguwar ta Wilma zata ratsa yankin tsibirin na Yukatan da kuma yammacin Cuba. Ko da yake karfin guguwar ya dan ragu, amma har yanzu tana tafiyar kusan kilomita 250 cikin awa daya.