Mahaukaciyar guguwa jamus | Labarai | DW | 18.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahaukaciyar guguwa jamus

Sakamakon mahaukaciyar guguwa data taso daga arewacin tarayyar jamus ayau,an dakatar da tashi da saukan jiragen sama.Kazalika wannan guguwar ta tilasata tsayar ta dukkan jiragen kasa daga zirga zirga a biranen arewaci da yammacin kasar,ayayinda aka rufe dukkan makarantu.Majiyar filin saukar jiragen sama dake birnin Frankfurt na nuni dacewa an soke tashin jiragen sama kimanin 122,kana a birnin Munich aka soke tashin jirage 16.Kawo yanzu dai mutum guda ne ya rasa ransa sakamakon kokarin dayake na kaucewa wata bishiya da guguwar ta tuge.Wannan mahaukaciyar guguwa ce ta gajerta ziyarar sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice a birnin Berlyn,inda ta gaggauta barin jamus zuwa birnin London.