1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manowa na cikin fargaba a Zamfara

Zainab Mohammed Abubakar
May 27, 2018

'Yan bindiga sun kashe mutane 27 a kauyen Gidan Goga na karamar hukumar Muradun a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yammacin Tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/2yQK6
Nigeria Angriff auf Mädchenschule in Dapchi
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Lamarin ya faru ne a lokacin da wasu mahara suka farwa manoma da suka je shuka a gonakinsu, suka kashe su nan take. Bayan nan al'ummar gari sun je daukar gawarwakin wadanda aka kashen, 'yan bindigar suka sake dawowa suka bude musu wuta.

Sai dai kokarin jin ta bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar ta Zamfara DSP Shehu Muhammad ta wayar tarho ya ci tura. Yanzu haka dai manoman wannan jiha na cikin fargaba ganin damina ta kama amma zuwa gona na neman gagararsu.