Mahamud Abbas ya dakatar tantanawa da Hamas a game da sabuwar gwamnati | Labarai | DW | 18.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahamud Abbas ya dakatar tantanawa da Hamas a game da sabuwar gwamnati

Shugaban hukumar palestinawa Mahamud Abbas, ya bayyana dakatar da shawarwari da ƙungiyar Hamas a game da batun girka gwamnatin haɗa ka.

Abbas ya ce ɓangarorin 2, sun shinfiɗa daftarin da zai girka wannan gwammnati da kuma mayan ayyukan da za ta gudanar, bayan kwanajki da dama na tantanwa.

To saidai ba a je ko ina ba, Praministan mai ci yanzu, Isma´il Hanniye na Hamas, ya hurta kalamomi, wanda kwata-kwata, su ka saɓawa yarjejeniyar da a ka cimma.

Mahamud Abbas ya ce, a lokacin tantanawar Hamas ta yi alkawarin amincewa da dukan yarjejeniyoyin da su ka gabata tsakanin Isra´ila da ƙungiyar PLO.

To amma daga bisani ƙungiyar, ta bayyana wani matsayi da ya saɓawa hakan.

A yanzu hakan shugaban hukumar Palestinawa na kann hanyar sa, zuwa birnin New York na ƙasar Amurika, inda zai halarci taron shugabanin ƙasashen Majalisar Ɗinkin Dunia.