Mahalarta taron Moscou sun watse baran-baran | Labarai | DW | 19.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahalarta taron Moscou sun watse baran-baran

An watse baran-baran a traon da aka gudanar jiya, a birnin Mosko na ƙasar Rasha, tsakanin ƙasashe 5 masu kujerun dindindin a komitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin dunia, da kuma Jamus a game da rikicin makaman nuklear Iran

Saidai, duk da saɓanin ra´ayoyin da a ka samu, mahalarta taron sun cimma daidaito,, a kan cewar ƙasar Iran ta wuce gona da iri.

Sannan, sun yi na´am, a kan wajibcin warware wannan rikici ta hanyar diplomatia , saɓanin ra´ayin gwanatin Amurika, na anfani da tsinin bindiga, domin ladabtar da hukumomin Teheran.

A jawabin da yayi jiya,shugaban ƙasar Amurika Georges Bush, ya sannar cewa a halin yanzu, matakin soja kaɗai ya rage, a ɗauka a kan Iran.

Wannan jawabi ya biwo bayan kalamomin shugaba Mahmud Ahmadi Nidjad ,inda ya hurta cewar Iran, shire ta ke, ta guntsera hannun duk wani ,wanda zai mata shishigi a harakokin ta, na cikin gida.