Mahalarta taron Annapolis sun isa Amirka | Labarai | DW | 26.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahalarta taron Annapolis sun isa Amirka

Shugaban Amirka George W Bush ya yi kira ga Isra´ilawa da Falasɗinawa da su kara mayar da himma a kokari cimma zaman lafiya tsakanin su. Kwanaki biyu gabanin taron ƙolin yankin Gabas Ta Tsakiya da zai guna a birnin Annapolis shugaba Bush ya ce ya na jin yana da alhakin ganin an cimma wata masalaha ta ƙasashe. A nasa bangaren shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas ya ce yana ganin taron a matsayin wani harsashin tattaunawar karshe ta kafa wata ƙasar Falasdinu. Shi kuwa Firaministan Isra´ila Ehud Olmert cewa yayi yana sa rai za´a yi tattauanwa mai ma´ana akan muhimman batutuwa. A halin da ake ciki Syria ta karbi goron gayyatar Amirka don halartar taron. Mukaddashin ministan harkokin wajen ta zai jagorancin tawagar ta zuwa gun taron. Syria ta yanke shawarar halatar taron ne bayan da aka amince a saka batun tuddan Golan cikin ajandar taron.