Mahajjata na kan hanya zuwa filin Arfa | Labarai | DW | 18.12.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahajjata na kan hanya zuwa filin Arfa

Mahajjata sama da miliyan biyu ne ke shirin gudanar da hawan arfa a ƙasa mai tsarki, a wannan rana ta Talata tara ga watan Dhul- Hajj. A yanzu haka dai maniyyatan na a kan hanyarsu ta zuwa duten na arfa. Hawan arfa dai na ɗaya daga cikin muhimman ayyukan aikin hajji. Tuni dai mahukuntan Saudiya su ka ɗauki tsauraran matakan tsaro, don tabbatar da doka da kuma oda. Ministan cikin gida na Saudiya, Yarima Nayef bin Abdulaziz, ya ce an ɗauki matakan ne don kare lafiyar maniyya, a lokacin gudanar da aikin hajjin. A gobe laraba ne idan Allah ya kaimu za a gudanar da Idin babbar Sallah.

 • Kwanan wata 18.12.2007
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Cd21
 • Kwanan wata 18.12.2007
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Cd21