Magunguna masu rafusa ga Afirka | Siyasa | DW | 06.04.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Magunguna masu rafusa ga Afirka

Kasashe da dama na Afurka kan sha fama da wahala wajen kiwon lafiyar al'umarsu saboda tsadar magunguna

A dai halin da ake ciki yanzu Krisana Kraisintu malamar harhada magunguna ‚yar usulin kasar Thailand na dab da cimma burinta na samar da magunguna masu rafusa ga mabukata a nahiyar Afurka. Ita kanta malamar ce ta kirkiro samfurin magungunan tare da fatan cewar zai taimaka wajen gabatar da jiyya ta gaggawa ga yara kanana. Babban abin da take fatan cimmawa shi ne magance matsalar zazzabin cizon sauro da kan halaka mutane kusan miliyan biyu a nahiyar Afurka a duk shekara, sai kuma tinkarar cutar nan ta kanjamau dake karya garkuwar jikin dan-Adam. Ra’ayin gabatar da magunguna masu saukin kudi ga majiyyata a nahiyar Afurka ya zo wa jami’ar mai shekaru 53 da haifuwa ne a shekarar 1990 lokacin da take shugabancin kamfanin harhada magunguna na gwamnatin kasar thailand. Ta ce kamfanin na GPO a takaice ya kan samar da isassun magunguna domin majiyyata sama da dubu 100, wadanda suka hada da majiyyata dubu 70 a Thailand da kuma wasu dubu 30 a Kamboja. A zamanin baya ta kan kashe abin da ya kai dalar Amurka 800 a kowane wata domin jiyyar marar lafiya daya kwal da magungunan da ta kan saya daga kasar Amurka. Amma tun bayan da ita kanta ta canza shawara domin harhada magungunan a cikin gida sai tsadar ta ragu zuwa dala 27 kacal akan kowane majiyyaci guda a wata. A yau an wayi gari kasar ta Thailand tana da ikon jiyyar dukkan masu fama da cutar kanjamau a kasar ba tare da ta shigo da ko da kwaya daya ta magani daga ketare ba. Wannan nasarar ce malamar harhada magungunan daga kasar ta Thailand take fatan ganin ta yadu zuwa sauran sassa na duniya. Ta fara daukar mataki akan wannan manufa a shekara ta 1999 domin gabatar da magungunan zazzabin cizon sauro masu saukin farashi a nahiyar Afurka. A wancan lokaci mahukuntan Thailand sun bayyana adawarsu da wannan shawara suna masu fifita harhada magungunan a cikin gida domin fitar da su zuwa nahiyar ta Afurka. A sakamakon haka Kraisintu da ajiye aikinta a shekara ta 2002, kuma tun daga sannan take kai da komo tsakanin kasashen Kongo da Benin da eritrea da Liberiya a kokarinta na ganin an gabatar da matakan harhada magungunan a wadannan kasashe. Ita ma kasar tanzaniya ta fara sha'awar shiga a dama da ita a wannan kyakkyawan ci gaba a harkar kiwon lafiya. Kraisinatu na samun goya-baya daga kungiyoyin taimako masu zaman kansu, abin da ya hada har da kungiyar action medeor ta nan Jamus, wacce ke da shirye-shiryen kiwon lafiya kimanin 9000 a kasashe 126.