1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Magu na EFCC ya sake kwato kudin haram

March 3, 2017

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa na ci gaba da kai samame a Najeriya, Inda ta tuhumi wasu kamfanonin hako mai na Shell da ENI da kokarin halarta kudaden haramun.

https://p.dw.com/p/2YbPv

A birnin Kaduna dai EFCC ta yi nasarar karbo motocin alfarma da dukiya mai dama. Sannan ta tsallaka Kano inda a can ma wasu gwalagwalan alfarma suka fada ya zuwa tarkonta. Ko bayan nan EFCC bata bar manyan kamfanoni hakar mai ba, wadanda yanzu haka take tuhuma da kokarin halarta dubban miliyoyi na daloli na haramun.

Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu ya sauya taku tare da kwato kudade daga hannun barayn karkashin sabon shirin tseguntawa. kusan daukacin hukumomin yaki da hancin tarrayar Najeriyar na dogaro ne ga taimako na kasashen waje domin iya aiwatar da ayyukansu cikin kasar. Abun da a cewar Auwal Musa Rafsanjani, shugaba na kungiyar Transparency in Nigeria mai fafutukar yakar cin hancin ke zaman barazana ga kokarin kai karshen annobar a cikin sauri.

Wata matsalar da ke kara fitowa fili dai na zaman ta barayin kasar ta Najeriyar da ke mai da martani ga yakin hancin mai zafi.
Abun kuma da ya kai ga gaza tabbatar da wanke shugaban hukumar a gaban majalisar dattawa inda dama a cikin 'ya'yanta ke fuskantar zargin cin hancin. Sai dai kuma duk da hakan a cewar Ibrahim Magu EFCC bata shirin sararawa duk da martanin barayi.