1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Magani daga tsirai don yaki da zazzabin cizon sauro

Alexa Meyer/ SBSeptember 9, 2015

Kamfanin API da ke Jamhuriyar Benin yana amfani da tsirai fiye da 50 wajen harhada magungunan yaki da zazzabin cizon sauro.

https://p.dw.com/p/1GTgW
Hoto: picture-alliance/epa/S. Morrison

Shekaru 25 da suka gabata an kafa kamfanin samar da magunguna ta amfani da tsirai a kasar Jamhuriyar Benin da ke yankin yammacin Afirka, wanda Valentin Agon yake jagoranta. Kamfanin ya taka mahimmiyar rawa musamman wajen samar da maganin yaki da zazzabin cizon sauro.

Jamhuriyar Benin dai kasa ce mai albarkatun tsirai. Wasu daga ciki kamfanin API yana amfani da su wajen samar da magunguna musamman na zazzabin cizon sauro.

Amfani da tsirai wajen sarrafa magunguna

Kamfanin API yana amfani da tsirai fiye da 50 wajen magunguna. Fasahar ta samu asali daga maganin gargajiya. Francois Djedatin ke zama shugaban kula da sarrafa maganin.

"A gare mu wannan wani lokaci ne mai daukar hankali a Afirka mummman a Benin, mun ga yadda ake samar da wadannan magunguna, da kuma sanin cewa muna da karfin fasahar samar da magunguna masu amfani, tare da samar da mafita ga matsalolin Afirka."

Gelber Chinarindenbaum
Hoto: picture alliance/blickwinkel/A. Jagel

Ya zuwa yanzu maganin API Palu na yaki da zazzabin cizon sauro. Ana amfani da shi a kasashe biyar na yammaci da tsakiyar Afirka da suka hada da Jamhuriyar Benin, da Jamhuriyar Nijar, da Burkina Faso, da Chadi, da kuma Jamhuiriyar Afirka ta Tsakiya. An samar wa mutane fiye da 300 aiki. A shekara ta 2014 kamfanin ya samu kimanin Euro 760,000.

Matsalar rashin hanyoyin mota masu kyau

Lokacin damina ana samun matsalar makalewar motoci masu dakon maganin a cikin tabo, saboda rashin kyaun hanya daga kamfanin mai nisa kilomita 100 da birnin Kwatanou. Kafin motocin su samu wucewa zuwa sauran kasashe.

Valentin Agon ya shafe shekaru 25 yana wannan aiki kuma shi ke jagorantar kamfanin:

"A Afirka yara 3000 ke mutuwa kowace rana daga cutar Malaria. Shin mai zai hana bincike, mai zai sa a jira sai wani ya zo daga wani wuri. Shi ya sa muka yanke shawarar cewa da kanmu za mu yaki cutar ta amfani da maganin gargajiya da iyaye da kakanni suka yi amfani da su tun da har yanzu."

Handy-App gegen Malaria EINSCHRÄNKUNG
Balaguro neman tsirai don sarrafa maganiHoto: Malaria Consortium

Ana sayar da maganin API a shagunan sayar da magani na Jamhuriyar Benin. Kamfanin na da irin wadannan shaguna kimanin 300 a kasar. Agon ya ce maganin Malaria ya kunshi tsirai ne babu wasu sinadarai. Sannan Valentin Agon shugaban kamfanin na API Benin ya kara da cewa:

“Ana sayar da na mu Euro daya da centi 50, na su kuma Euro 10. Sannan na mu daga halittu ne. Mun yi daga tsirai. Na su daga sinadarai. Mutane sun fi son ma'ammala da tsirai."

Idan ana bukatar sanin mahimmancin wannan farashi sai a duba yadda rayuwa take a birnin Kwatanou cibiyar kasuwancin kasar ta Jamhuriyar Benin inda matsakaicin ma'aikaci yake samun albashi kimanin Euro 1.300 a shekara.