Maganar Sudan Na Ci Gaba Da Mamaye Kanun Rahotannin Jamus Akan Afurka | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 28.05.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Maganar Sudan Na Ci Gaba Da Mamaye Kanun Rahotannin Jamus Akan Afurka

Daya daga cikin batutuwan da jaridun Jamus suka yi sharhi akansa a wannan makon shi ne bikin kama aikin kwamitin tsaron zaman lafiyar Afurka ta aka gabatar a Addis Ababa, wanda kuma jaridun ke ganin cewar rikicin Sudan ka iya zama zakaran gwaji ga ayyukansa

Har yau kasar Malawi na ci gaba da fama da talauci

Har yau kasar Malawi na ci gaba da fama da talauci

Daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin masaharhanta na jaridun Jamus a wannan makon har da bikin da aka gabatar na kama aikin kwamitin tsaron zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Afurka a birnin Addis Ababa. A lokacin da take gabatar da rahoto game da haka jaridar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

"Manufar kafa wannan kwamiti na tsaro da Kungiyar Tarayyar Afurka (AU) Shi ne domin daukar nagartattun matakai na kadagarki da kuma tinkarar rikice-rikice da yake-yake na basasa da kashe-kashe na kare dangi a nahiyar Afurka. Akwai kudurin katsalandan soja da aka tanadar ko da kuwa tare da bacin ran kasar da lamarin ya shafa. Kasar Sudan kuwa ka iya zama zakaran gwaji dangane da wannan manufa."

Rikicin kasar ta Sudan ta ci gaba da mamaye kanun rahotannin jaridun Jamus a wannan makon ta la’akari da mawuyacin halin da ake ciki da kuma barazanar karatowar yanayin damina yadda al’amura zasu dada rincabewa muddin ba a samu kafar kai taimakon gaggawa ga mutanen da lamarin ya shafa ba. A lokacin da take sharhi game da haka jaridar DIE WELT ta bayyana mamakinta a game da Kungiyar hadin Kan Larabawa da ta kasashen Musulmi suka zura ido suna kallon ta’asar dake faruwa a yankin Darfur ba tare da sun ce uffan ba, alhali kuwa musulmi ne ke yakar musulmi ba gaira-ba-dalili. Jaridar sai ta kara da cewar:

"Wannan tasar dake samun goyan baya daga shugaban kasar Sudan Umar Hasan Al-Bashir abu ne dake nunarwa a fili cewar a baya ga fafutukar yada tsattsaurar akida ta addini, gwamnatin Sudan kazalika tana bin wasu manufofi na wariyar jinsi a yake-yaken basasar dake addabar kasar. Domin kuwa abokan gabar da ake fatattaka a lardin Darfur Musulmi ne, amma fa bakar fata ne ba Larabawa jajayen fatu ba. Ga alamu wannan shi ne ainifin dalilin da ya sanya Kungiyar Hadin Kan Larabawa ta zura na mujiya tana kallon abin dake faruwa ba tare da ta ce uffan ba."

A makon da ya gabata ne aka gudanar da zaben shugaban kasa a Malawi ta kudancin Afurka. Jaridar DIE TAGESZEITUNG tayi amfani da wannan dama domin bitar tarihin kasar da kuma halin da take ciki yanzun. Jaridar sai ta ci gaba da cewar:

"Bayan sama da shekaru talatin da tayi tana karkashin mulkin kama karya na Dr. Hastings Banda, kasar Malawai ta samu sabon shugaba, wanda aka nada sakamakon zaben demokradiyya da aka gudanar karo na farko a kasar a shekarar 1994. To sai dai kuma duk da wannan kyakkyawan ci gaba da aka samu Malawi ta ci gaba da fama da matsaloli na yunwa da talauci, inda kimanin kashi 50% na al’umarta ke samun abin da ya gaza Euro daya a rana. A baya ga haka gaggan kasashe mawadata dake da ci gaban masana’antu sun dakatar da taimakon rayawar da suke ba wa Malawin dangane da matsalar cin hanci da rashin bin nagartattun manufofin tattalin arziki. Wani abin da ya kara tsananta lamarin kuma shi ne yaduwar cutar nan ta AIDS tsakanin al’umar wannan kasa, inda alkaluma suka nuna cewar a yanzu haka kimanin kashi 12% ne daga cikinsu ke dauke da kwayoyin cutar mai karya garkuwar jikin dan-Adam."

A can kasar Namibiya gwamnati ta ba wa manoma farar fata zabi ko dai su sayar da wani bangare na gonakinsu ko kuma gwamnati ta kwace karfi da yaji. Jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU tayi bitar lamarin sai ta kara da cewar:

"Duk da wannan barazanar da gwamnati ta gabatar, wacce ga alamu take da nasaba da manufar nada wani dan takarar da zai wakilci jam’iyyar SWAPO a zaben shugaban kasar Namibiya da za a yi a cikin watan nuwamba mai zuwa, amma ofishin jakadancin Jamus a Windhuk ba ya zaton cewar za a fuskanci wata matsala irin shigen ta kasar Zimbabwe. Domin kuwa gwamnati ta sha nanata cewar za a yi biyayya ne sau da kafa ga abubuwan da doka ta tanadar domin warware matsalar ta rabon filayen noma a kasar Namibiya. Hakan kuwa na ma’ana ne cewar duk wani manomin da aka kwace gonarsa yana da ikon daukaka kara gaban kotu da kuma neman biyansa diyya."