1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mafi yawan alummar Izraela na bukatar Olmert yayi murabus

Kashi 63 daga cikin 100 na alummar kasar Izraela ,sun bukaci prime minista Ehud Olmert yayi murabus daga mukaminsa,saboda yadda yake tafiyar da batun yakin kasar lebanon.Akasarin yan izraelan dai na ganin yakin da dakarun kasar suka gwabza da yan hizbollah,tankar babbar asara ce ,domin sojoji biyu da aka cafke daga bangaren izraelan,a ranar 12 ga watan daya gabata wanda shine ya haifar da wannan yaki,har yanzu sun hannun yan hizbollah ,kana shugabancin kungiyar na nan.Akalla Lebanawa 1,110 da yahudawan Izraelan 157 ne suka rasa rayukansu ,a wannan rikici na yini 34.Yahudawan Izraelan dai na bukatar premier Olmert ,dayayi koyi da Meir,wanda aka tilastawa yin murabus a yakin yankin gabas ta tsakiya na 1973,yakin da masar da syria suka samu nasaran daya haddasawa izraelan asara mai dumbin yawa.

 • Kwanan wata 25.08.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5l
 • Kwanan wata 25.08.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5l